Kansila da Wani Mutum Guda Sun Mutu a Wani Rikicin Kabilanci a Ondo

Kansila da Wani Mutum Guda Sun Mutu a Wani Rikicin Kabilanci a Ondo

  • Wasu tsagerun matasa ɗauke da bindigu sun kashe Kansila da wani mutun daya a kauyen Koresu, karamar hukumar Odigbo jihar Ondo
  • Bayanai sun nuna cewa harin wanda ake zargin matasan Ikale da kai wa ya biyo bayan harbin wata mata a a ƙauyen Kajola
  • A cewa kwamandan Amotekun kuma hadimin gwamna kan tsaro, mutanen yankunan biyu sun jima ba su ga maciji

Ondo - Mutane biyu sun rasa rayukansu a ƙauyen Koresu, yankin manoma a ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo lokacin da wasu ɗauke da bindigu suka kai harin ɗaukar fansa.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da Kansila mai wakiltar yankin da kuma wani Ɗan Banga da aka gano sunansa Kayode.

Taswirar jihar Ondo.
Kansila da Wani Mutum Guda Sun Mutu a Wani Rikicin Kabilanci a Ondo Hoto: thenation
Asali: UGC

Har yanzun ba'a gano ainihin sunan Kansilan ba. An tattaro cewa yan bindigan sun kai harin ne ranar Asabar sakamakon harbe wata mata a kauyen Kajola, ƙaramar hukumar Okotipupa.

Kara karanta wannan

Dalilin da Ya Sa Nake Goyon Bayan Tinubu Duk Ba Jam'iyyar Mu Ɗaya Ba, Sanatan PDP Ya Faɗi Abinda Ya Hango

'Yan bindigan waɗanda ake zargin matasan Ikale ne sun yi kaca-kaca da gonakin mutanen ƙauyen. Wani mai suna Christiana Umukoro, ya tabbatar da harin yace mahaifinsa ya ci duka a hannun maharan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa kusan kashi 95 cikin 100 na mazauna ƙauyen sun tsere domin ceton rayuwarsu.

Mashawarci na musamman ga gwamna Oluwarotimi Akeredolu kan harkokin tsaro kuma kwamandan Dakarun Amotekun, Chief Adetunji Adeleye, yace tuni aka kai gawarwakin mutanen biyu ɗakin ajiyar gawa.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Adeleye, wanda ya musanta kashe dakarun Amotekun a harin, yace komai ya koma dai-dai a ƙauyen. Yace an jigbe sojoji, yan sanda da jami'an Amotekun a ƙauyen.

A cewarsa, "Akwai wata tsohuwar gaba tsakanin iyalan Oluku na Ikale a Okotipupa da manoman Oyo/Osun dake zaune a ƙaramar hukumar Odigbo."

"Mutanen Oyo/Osun manoma hatsi ne kuma suna faɗa da juna ne kan mallakin gonaki. Wannan sabuwar rigimar ta kunno ne bayan an harbi wata mata 'yar Kajola."

Kara karanta wannan

Tsohon Mataimakin Gwamna, Shugaban Matasan PDP Na Shiyya da Wasu Jiga-Jigai Sun Koma APC

"Muna zargin matasan Ikale suka kai harin ɗaukar fansa kan manoman, an kashe Kansilan yankin Oyo/Osun kana an kashe Ɗan Banga ɗaya ba wai ɗan Amotekun ba."

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan jihar Osun, SP Funmilayo Odunlami, tace babu ɗan sandan da harin ya shafa kuma nan ba da jimawa ba hukumar zata fitar da bayanai.

A wani labarin kuma Kwamandojin Boko Haram Da Suka Tuba Sun Fadi Wani Sirri da Shekau Ya Bari Kafin a Sheke Shi

Wasu daga cikin yan ta'addan ƙungiyar Boko Haram da suka zubar da makamansi sun bayyana wasu abubuwa da suka shafi tsohon shugabansu, Abubakar Shekau.

A cewarsi tubabbun yan ta'addan, Shekau ya mutu ya bar kwarkwara sama da 80. Idan baku manta ba kungiyar ISWAP ce ta yi ajalin Abubakar Shekau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262