FAAN Ta Dauki Matakin Gaggawa da Gobara Ta Tashi a Filin Jirgin Saman Legas

FAAN Ta Dauki Matakin Gaggawa da Gobara Ta Tashi a Filin Jirgin Saman Legas

  • Gobara ta tashi a bangaren filin jiragen saman Murtala Muhammad (MMIA) da sanyin safiyar yau Alhamis, 25 ga watan Afrilu
  • Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta karkatar da dukkanin ayyukan jiragen sama daga bangaren
  • FAAN a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Misis Obiageli Orah ta zargi tartsatsin wutar lantarki da haddasa gobarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta karkatar da dukkanin ayyukan jiragen sama a bangaren E na filin jiragen saman Murtala Muhammad (MMIA).

Gobara ta tashi a filin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas
Hukumar FAAN ta tabbatar da tashin gobara a filin jiragen sama na Legas, ta fara bincike. Hoto: Murtala Muhammad Airport
Asali: Facebook

Hakan ya biyo bayan wata gobara da ta tashi a tashar da sanyin safiyar yau Alhamis bayan da aka samu fitar hayaki a gadar filin mai lamba E54.

Kara karanta wannan

Jami'ar Najeriya ta dauki mataki kan malamin da aka kama yana lalata da daliba

Filin jirgin ya sha fama da gobara

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa jami’an hukumar ceto da kashe gobara na filin (ARFFS) sun yi gaggawar daukar matakan shawo kan gobarar tare da katse wutar lantarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa tsohuwar tashar filin jiragen saman ta dade tana fuskantar iftila'i na gobara, wanda hakan ya sa aka rufe ta na wani lokaci.

FAAN a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Misis Obiageli Orah, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’an kashe gobara na filin jirgin sun yi abin da ya dace.

"Tartsatsin lantarki ya haddasa gobarar" - FAAN

A cikin sanarwar da jaridar The Cable ta gani, Orah ta ce:

"Da misalin karfe 05: 29 na safiya aka gano hayaki yana tashi daga gadar E54, wanda ya tilasta injiniyoyi katse wutar lantarkin daukacin bangaren E.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta dakatar da duka jiragen kamfanin Dana Air daga aiki

“Rundunar ceto da kashe gobara ta filin jirgin saman (ARFFS) ta yi gaggawar kai dauki inda abin ya faru, kuma sun isa wurin da karfe 05:30 na safe.
Muna kyautata zaton tartsatsi daga na'urar rarraba lantarki ne musabbabin gobarar, amma muna ci gaba da bincike domin gano gaskiyar dalilin tashin wutar."

An dakatar da ayyukan jirgin Dana Air

Idan ba a manta ba, a jiya Laraba ne Legit Hausa ta ruwaito ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya ba da umarnin dakatar da ayyukan kamfanin Dana Air.

An gano cewa wani jirgin Dana Air da ya taso daga Abuja dauke da daruruwan mutane ya kwace a lokacin da ya sauka filin jiragen sama na Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel