Jonah Jang yana alfahari da zuwa gidan yari, ya ce ya kafa wata tarihi

Jonah Jang yana alfahari da zuwa gidan yari, ya ce ya kafa wata tarihi

Tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Jonah Jang ya bayyana cewa ya kasance yana barci ne a gadon da tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Aremu Obasanjo ya kwanta a kai lokacin da aka kulle shi a gidan yarin Kuje da ke Jos.

Jang ya sanar da hakan ne yayin da yake karanto wata jawabi ta bakin tsohon kwamishinan yadda labaransa, Pastor Abraham Yiljap da ya wakilce shi a bukin General Church of Christ in Nations (COCIN) da kayi a yau Laraba.

Jonah Jang yana alfahari da zuwa gidan yari, ya ce ya kafa tarihi
Jonah Jang yana alfahari da zuwa gidan yari, ya ce ya kafa tarihi

A sakon fatan alkhairi da ya aike wa cocin, Jang ya ce garkame shi da akayi a gidan yari iko ne na Allah saboda haka babu wanda ya isa ya rika cika bakin cewa ya tura shi gidan kurkuku.

KU KARANTA: Abin kwaikwayo ne: An sace sandan ikon majalisar Jihar Gombe

"Shiga na kurkuku darasi ne da ya kara min kankan da kai, a lokacin da na ke ofishin EFCC a Abuja, a kasa na ke kwana amma a gidan yarin, na samu alfarma kwanciya a gadon da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kwanta a kai lokacin da ya ke gidan yarin Jos"

An garkame Jonah Jang bisa zarginsa da aika laifuka 12 masu alaka da rashawa da karkatar da kudi N6.3 biliyan a lokacin da ya ke gwamnan jihar Filato. Sai dai a yau, an bayar da belin Jang bayan kotu ta bukaci ya gabatar da mutane biyu da zasu tsaya masa tare da mika fasfo dinsa na fita kasashen waje.

Gwamna mai ci yanzu, Simon Lalong shima ya ce ya taba shiga gidan kurkukun inda ya kwashe kwanaki 40. Gwamnan ya fadi hakan ne a jawabin da ya yi wajen bude taron COCIN karo na 94 da aka gudanar a Jos.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164