Jerin Alkalan Alkalai na kasa da aka yi a tarihi tun daga 1958-2022, da yadda suka kare

Jerin Alkalan Alkalai na kasa da aka yi a tarihi tun daga 1958-2022, da yadda suka kare

  • Mun kawo jerin duka Alkalin Alkalan da suka jagoranci babban kotun koli bayan samun ‘yancin kai
  • Daga ciki za a ji cewa akwai wadanda aka nemi a kora daga aiki, da wadanda suka yi murabus domin kansu
  • Mafi yawan Alkalan Alkalan da aka yi, sun dauki tsawon lokaci su na bakin aiki kafin su kai ga ritaya

1. Adetokunbo Ademola

Mai shari’a Adetokunbo Ademola ya yi shekara kusan 15 yana rike da kujerar Alkalin Alkalai. Bayan ya bar kujerar a 1972, ya rike shugabancin hukumar kidaya ta kasa.

2. Taslim Olawale Elias

Tsakanin 1972 – 1975, Taslim Olawale Elias ne shugaban Alkalan Najeriya. An tunuke shi bayan juyin-mulkin da sojoji suka yi, amma daga baya sai ya koma kujerar shari’a.

Kara karanta wannan

Al-Mustapha: A Shirye Na Ke In Mutu Domin 'Yan Najeriya

Taslim Elias ya yi aikinsa lafiya kau, shi ne ‘dan Najeriya da ya fara zama a babban kotun Duniya. A lokacin yana aiki kotun koli, ya cigaba da zama malami a jami’ar Legas.

3. Frederick Rotimi Alade Williams

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lauyan Najeriya da ya fara zama SAN a tarihi shi ne Rotimi Atanda Fatai Williams, SAN CFR, CON, GCFR, ya zama CJN ne a shekarar 1979, a shekarar 1983 ya yi ritaya.

Kafin nan, Rotimi Fatai Williams ya taba rike shugaban kungiyar Alkalai na kasa a shekarar 1959.

4. George Sodeinde Sowemimo

Tarihi ba zai manta da da George Sodeinde Sowemimo wanda ya zama Alkalin Alkalai a Najeriya a 1983, bai sauka ba sai a 1985. Sowemimo ya bar Duniya yana 77 a 1997.

5. Ayo Gabriel Irikefe

Mai shari’a Ayo Gabriel Irikefe ne wanda ya shugabanci Alkalan kotun koli bayan RFA Williams. Irikefe ya yi mulki daga 1985 zuwa 1987, a lokacin ana yin ritaya a shekara 65.

Kara karanta wannan

Bincike ya nuna dukiyar Attajirai 2 za ta iya fito da mutum miliyan 63 daga talauci

6. Mohammed Bello

Mutumin Arewa da ya fara zama CJN shi ne Mohammed Bello a 1987. Mai shari’a ya yi suna a kotun koli, ya yi ritaya a 1995, daga baya ya rasu a daf da karshen shekarar 2004.

7. Muhammad Lawal Uwais

A 1995 Mohammed Lawal Uwais ya hau kujerar Alkalin Alkalai na kasa. Bayan ya yi ritaya a shekarar 2006, ya jagoranci kwamitin da ya yi aikin gyaran harkar zabe a Najeriya.

8. Salihu Modibbo Alfa Belgore

Bayan tsawon shekaru 20 a kotun koli, Alfa Belgore ya zama Alkalin Alkalai a Yulin 2006. Bai dade ba ya yi ritaya daga aiki a Junairun 2007 a dalilin cika shekara 70 a Duniya.

Tanko Mohammed
Tsohon Alkalin Alkalai na kasa, Tanko Mohammed
Asali: Twitter

9. Idris Legbo Kutigi OFR, GCON

Idris Legbo Kutigi ya samu karin matsayi zuwa Alkalin kotun koli a 1992, shi ya canji Alfa Belgore a kujerar CJN, ya yi shekaru kusan uku kafin shi ma ya cika shekarun ritaya.

Kara karanta wannan

Tsohon Alkalin Alkalai zai tashi da Naira Biliyan 2.5 bayan ya yi murabus daga ofis

Da ya bar kotun koli, Mai shari’a Idris Legbo Kutigi ya cigaba da aiki a kotun tarayya har ya rasu.

10. Aloysius Iyorgyer Katsina-Alu

Tun farko Idris Kutigi ya rantsar da Aloysius Iyorgyer Katsina-Alu a 2009 saboda Shugaba Ummaru Yaradua bai da lafiya. Da ya cika shekara 70, ya yi ritaya salin-alin a 2011.

11. Dahiru Musdapher

Bayan aikin da ya yi a Kano da kotun daukaka kara, Dahiru Musdapher ya je kotun koli a 2003. A 2011 ya zama CJN, ya yi shekaru uku yana jagorantar kotun koli, har ya ajiye aiki.

12. Aloma Mariam Mukhtar

A 2012 ne aka kafa tarihi a shari’ar Najeriya, Aloma Mariam Mukhtar ta zama macen farko da ta zama Alkaliyar Alkalai, ta shugabanci kotun koli har zuwa ritayarta a 2014.

13. Mahmud Mohammed

Mahmud Mohammed ya zama Alkalin babban kotun kasar nan ne a 2005. Bayan shekara tara ya yi dacen zama zama sabon Alkalin Alkalai kuma shugaban majalisar NJC a 2014.

Kara karanta wannan

Zawarcin Kwankwaso Ya Koma APC: NNPP Ta Yi Wa Jam'iyyar APC Kaca-Kaca

14. W.S. Nkanu Onnoghen

Shi ma W.S. Nkanu Onnoghen ya zo kotun koli ne a 2005, ya zama CJN na rikon kwarya a 2016, daga baya an tabbatar da shi. Dole ya yi murabus a 2019 saboda zargin rashin gaskiya.

15. Tanko Ibrahim Mohammed

Shi ma Tanko Ibrahim Mohammed ya bi sahun Walter Onnoghen, inda ya rubuta takardar murabus a 2022. Mai shari’an ya ajiye aiki ne alhali lokacin ritayansa bai ba tukuna.

Tanko ya bar aiki

Kun ji labari cewa Tanko Muhammad yana da ragowar shekara da rabi da ya rage masa a ofis, amma ya rubuta takardur murabus na ajiye aiki a watan Yunin 2022.

Ana zargin cewa Mai shari’a Muhammad ya dade bai da cikakkiyar lafiya, yana fuskantar matsalar mantuwa da ta hana shi yin aikin alkalanci da kyau a kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel