Majalisar dokoki jihar Zamfara ta kirkiri sabuwar masarauta

Majalisar dokoki jihar Zamfara ta kirkiri sabuwar masarauta

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta zartar da kudirin neman kirkirar sabuwar masarauta a jihar.

A ranar Laraba ne majalisar ta amince da kudirin da aka gabatar a gaban ta na neman kirkirar sabuwar masarautar Bazai.

Amincewa da kirkirar sabuwar masarautar ya kawo jimillar masarautu a Zamfara zuwa 18.

A ranar Talatar da ta gabata ne, Ibrahim Kwatarkwashi, dan majalisa mai wakiltar mazabar Bungudu ta Gabas, ya mika rahoton kwamitin sa na neman kirkirar masarautar da sarakunan ta.

Kudirin ya samu tsallake karatu na biyu da na uku a zauren majalisar bayan Abubakar Gumi, mataimakin shugaban majalisar, ya karanta wa mambobin majalisar.

An kirkiri sabuwar Bazai ne daga masarautar Shinkafi.

A cewar dokar da majalisar ta zartar, za a daga darajar babban hakimin Jangeru a masarautar Shinkafi zuwa sarkin Yanka mai daraja ta uku, yayin da za daga darajar Kayayen Marafa zuwa hakimi a masarautar Talata-Mafara.

Gumi ya bawa magatakardar majalisa umarnin ya sanar da bangaren zartarwa domin gaggauta a hannu a kan dokar.

A kwanakin baya ne majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudirin tsaga masarautar jihar zuwa gida biyar.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada sabbin sarakunan yanka hudu a Kano cikin kasa da sa'o'i 48 bayan majalisa ta zartar da dokar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel