Za a Fara Bawa Malaman Makarantun Allo Shaidar Karatu Ta ‘NCE’ a Kaduna

Za a Fara Bawa Malaman Makarantun Allo Shaidar Karatu Ta ‘NCE’ a Kaduna

- Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti da zai yi aiki kan yadda za a yi wa makarantun allo garambuwul a gwamutsa su cikin makarantu na zamani

- Kwamishinan ilimi na jihar, Dr Shehu Muhammad ya ce kwamitin za ta fito da tsarin horaswa ga malaman allon ta yadda za su rika samun shaidar karatu ta malanta wato NCE

- Dr Muhammad ya ce an samar da wannan tsarin ne a matsayin mafita ta yadda almajiran za su samu ingantaccen ilimi su cigaba da makaranta ta frimare da sakandare don samun rayuwa mai inganci

Gwamnatin jihar Kaduna, a ranar Litinin, ta kafa wata kwamiti da zai samar da tsari na karatu domin bawa malaman makarantar allo shaidar koyarwa a jihar, Vanguard ta ruwaito.

Dr Shehu Muhammad, kwamishinan Ilimi na jihar, wanda ya kaddamar da kwamitin a Kaduna ya ce karkashin sabon tsarin, malaman makarantun allo za su rika samun takardan shaidar malanta ta NCE.

Za a Fara Bawa Malaman Makarantun Alo Shaidar Karatu Ta ‘NCE’ a Kaduna
Za a Fara Bawa Malaman Makarantun Alo Shaidar Karatu Ta ‘NCE’ a Kaduna. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Rashin Tsaro: Masu Zanga-Zanga Sun Rufe Manyan Tituna a Zamfara

Muhammad ya ce wannan matakin na cikin shirin da ake yi ne na yi wa karatun na tsangaya garambawul domin gwamutsa shi cikin tsarin ilimi tamkar na boko.

Ya bayyana karatun na almajiranci a matsayin tsari inda yaran musulmi masu kananan shekaru ke koyan ilimomi na addinin musulunci da tarbiya.

Kwamishinan ya ce duk da cewa musulmi har yanzu suna sha'awar tsarin, wasu sun bijiro da matsaloli cikinsa don haka akwai bukatar yi wa tsarin garambawul don ya dace da zamani.

"An dora wa kwamitin alhakin fidda tsari da zai samar da malaman makarantun allo da za su samu NCE kuma a iya daukansu aiki a makarantun frimare da sakandare.

"Kwamitin zai kuma samar da tsari ba bada horaswa ga malaman makarantun allo a jihar.

"Ana kuma sa ran kwamitin ya samar da tsarin yadda za a shigar da malaman makarantun allo zuwa tsarin koyarwa na zamani.

KU KARANTA: Masarautar Lapai Ta Tuɓe Wa Dagaci Rawani a Jihar Niger

"Idan an kammala, za a mika tsarin ga hukumar ilimin kwalleji na kasa domin dubba yiwuwar amfani da shi a matakin kasa," in ji shi.

Muhammad ya ce duk da cewa mafi yawancin malaman allo sun samu horasawa, sun haddace Al-Kurani, suna kuma da ilimin addinin musulunci, ba su da shaidar karatun da za a iya daukarsu aiki.

Ya ce an bawa kwamitin makonni shida don kammala aikinta.

A wani labarin daban, Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon.

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Asali: Legit.ng

Online view pixel