Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta

Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta

- Wani magidanci ya halaka babban limami bayan ya kama shi da matarsa a gado

- Magidancin ya ce matarsa ta fada masa za ta shiga ban daki ne a gidan makwabta amma ta tafi suka hade da limamin

- Magidancin ya ce ya shiga gidan makwabtan neman matarsa ya kuma ganta tare da liman zigidir amma ya tafi ya kyallesu

- Daga bisani bayan ya yi kararsu wurin yayansa, limamin ya kira shi tattaunawa amma suka fara cacan baki sai ya daba wa liman karfe a wuya

Babban limamin garin Enagi, Alhaji Attahiru Alhassan ya rasu bayan an daba masa wuka saboda zarginsa da badala da matar wani mutum mai suna Umaru Jibrin.

Jibrin, mai shekaru 35 ya kama babban limamin mai shekaru 48 ne da matarsa a gado a gidan makwabtansu, Daily Trust ta ruwaito.

Miji ya kashe limami bayan kama shi da matarsa a gado a gidan maƙwabta
Miji ya kashe limami bayan kama shi da matarsa a gado a gidan maƙwabta. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Jibrin, wanda aka yi holensa a hedkwatan yan sanda a Minna, babban birnin jihar, a ranar Talata ya bada labarin abinda ya faru a ranar da ya kama limamin da matarsa.

Ya ce limamin ya wuce shi ya shiga gidan makwabtansa da matarsa tunda farko ta ce masa zata shiga ban daki a bayan gidan.

Ya yi bayanin cewa bayan kimanin awa daya ya shude bai ga matarsa ba, ya tafi nemanta kuma ya ji muryarta a gidan makwabta.

"Na shiga na ga babban limamin da matata zigidir a kan gado. Suna kwance tare. Ban aikata komai ba. Na bar su na tafi gidan dan uwana na fada masa abinda na gani," in ji shi.

Jibrin ya ce ya fusata ne a lokacin da babban limamin ya kira shi domin tattaunawa kan batun.

"Yayin tattaunawa, musu ya yi zafi, sai na kwace karfen da ke hannunsa da karfi na daba wa babban limamin a wuya"

Hakan ya yi sanadin rasuwar limamin kuma Jibrin ya tsere amma an kama shi a kauyen Batati a karamar hukumar Lavun a jihar.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa shi ya halaka limamin amma saboda fushi.

Ya ce an fara bincike kuma nan gaba za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel