Sojin sama ta dawo da shirin daukar daliban sakandare kai tsaye zuwa aikin soja

Sojin sama ta dawo da shirin daukar daliban sakandare kai tsaye zuwa aikin soja

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta halarci taron yaye daliban makarantar sojin sama da ke Jos
  • Rundunar ta sanar da cewa, ta dawo da shirin daukar daliban sakandare kai tsaye zuwa sojin sama
  • Rundunar ta ce tuni wasu daliban da suka nuna sha'awa ga aikin sun shiga aikin sojin saman

Jos - Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) ta sake gabatar da shirin daukar daliban da suka kammala makarantar sakandare ta soji kai tsaye a matsayin sojan sama, The Guardian ta ruwaito.

Babban Hafsan Sojojin Sama (CAS), Air Marshall Isiaka Amao ne ya bayyana hakan, a wurin faratin yaye dalibai na 36 na Makarantar Sojojin Sama da ke Jos ta Jihar Filato.

Rundunar sojin sama sake dawo da shirin daukar daliban sakandare kai zuwa aikin soji
Daukar aikin sojin sama kai tsaye daga makarantar sakandaren sojin sama | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Amao ya ce wasu daga cikin daliban da suka nuna sha’awa kafin su shiga cikin shirin daukar kai tsaye an tura su rundunonin NAF daban-daban a fadin kasar bayan sun sami horo a Cibiyar Horar da Sojoji da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

NAF ta karyata rahoton biyan 'yan bindiga N20m don kada su harbo jirgin Buhari

AVM Isa Muhammad wanda ya wakilce shi, hafsan sojan ya umurci dalibai da su kiyaye tarbiyya mai kyau da suka koya yayin da suke makarantar sakandare, da kuma wadanda za su koya a aiki, don ba su damar kiyaye abubuwan da NAF ke bukata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

“POP na nuna kammala karatun ku na sakandare bayan shekara shida na horarwar ilimi da aikin soji a Makarantar Sojojin Sama. Makarantar ta yaye dalibai sama da 4,300 zuwa yanzu tun lokacin da aka kafa ta."

sta ruwaito cewa, jami'in ya kuma shawarce su da su zama masu jajircewa da kuma ba da gudunmawar da ake bukata don kare kasar.

Sojoji na gina rugar Fulani a kudu: Rundunar soji ta yi martani kan jita-jita

A wani labarin, Rundunar sojin Najeriya ta karyata jita-jitar da ke yawo mai cewa, a halin yanzu wata runduna na gina matsugunar Fulani a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi wa tsoffin sojojin Biyafara 102 afuwa, ya amince da biyansu kudin sallama

Jita-jitar da ake yadawa ta ce, runduna ta 82 ta sojin Najeriya tana aikin gina rugar Fulani a tsakanin Ochima da Affa a cikin Igbo-Etiti da Udi na jihar Enugu.

A cikin wata sanarwar da Legit.ng Hausa ta samu a ranar Laraba 13 ga watan Oktoba dauke da sa hannun Manjo Abubakar Abdullahi, Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Rundunar, rundunar sojin Najeriya ta watsi da batun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel