Kallo ya koma sama: Yar aiki ta lakaɗa ma Uwardakinta dukan tsiya, ta shiga halin rai fakwai mutu fakwai

Kallo ya koma sama: Yar aiki ta lakaɗa ma Uwardakinta dukan tsiya, ta shiga halin rai fakwai mutu fakwai

Wani al’amari bai ban tausayi ya faru a jihar Legas, inda wata yar aiki ta yi ma Uwardakinta ba zata, inda ta lallasa mata duka tare da fasa mata kwalba a kai, wanda a yanzu haka tana kwance a Asibiti cikin mawuyacin hali.

Jaridar Punch ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Litinin 5 ga watan Maris, a ranar da yar aikin mai suna Susan Samson yar asalin garin Kalaba ta nemi kashe uwardakinta mai suna Mistura a gidansu dake unguwar Ejigbo na jihar Legas.

KU KARANTA: Yan KAROTA sun ci na jaki a hannu direbobin A daidaita sahu a sakamakon wani hatsari da suka ja

Majiyar Legit.ng ta ruwaito lamarin ya samo asali ne tun bayan da Mistura ta dauki hayar Susan da nufin taimaka mata da akin gida, wato boyi boyi a ranar 4 ga watan Feburairu, sai dai zaman nasu ya fara rashin dadi ne a lokaci da uwargida Mistura ta fara zargin Susan da yi mata sata.

Da satar yayi yawa, sai Mistura ta shiga bincike, inda ta gano kudaden da ake zargin an sace zube a cikin jakar yar aikin, hakan ya sanya Mistura ta kira mutumin da ya kawo mata yar aikin, don ta fada msa abinda Susan ke musu a gidan.

Ganin dubunta ya cika, sai yar aikin ta yi kokarin tserewa, inda ta lallaba zuwa dakin uwardakinta, ta tarar da ita tana barci, daga nan sai ta dauki yaji ta zuba ma matar, daga nan kuma ta dauki kwlaba ta dinga dankara mata a kai har sai da ta suma.

Sai dai yar aikin bata samu cimma burinta na tserewa ba, har lokacin da makwabta suka jiyo ihun matar kafin ta suma, nan da nan suka fado gidan suka cika hannu da yar aikin, bayan suna lakada mata dan banzan duka, daga nan kuma suka mika ga ofishin Yansanda.

Har zuwa lokacin hada rahoton nan, uwargida Mistura na kwance cikin mawuyacin hali a Asibiti, bayan an yi mata tiyata tare da kara mata jinni leda 6, sakamakon rauni da ta samu a kwakwalwa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng