Waiwaye: Hanyoyin sadarwa a kasar Hausa na gargajiya
- A kasar Hausa dai, kafin zuwan turawa, akwai hanyoyin sadarwa da dama da ake amfani dasu
- Sadarwa na da amfani don isar da sako ga jama'a
- Kafafen sadarwa na zamani, sun ture na baya domin ingancinsu
A kasar Hausa a zamunna da suka shude, ana amfani ne da kafafen sadarwa ne wajen yada bayanai, sanarwa da isar da sakon hukuma ko masarauta ga talakawansu.
A wadancan lokuta, babu lantarki, babu yanar gizo, babu jirage, ba kuma kowa ne ya iya rubutu ba, balle karatu, don haka, magana ta fatar baki ita take iyar da sakonni.
A wasu lokuta akan kada kayan kida ko amsa kuwwa, domin a jawo hankalin mutane ga sakon da ake son bayarwa. Ga kadan daga cikin irin ababen da ake amfani dasu a kasar Hausa.
DUBA WANNAN: Janar Babangida yayi kra ga shugaba Buuhari da ya hakura a 2019
1. Amsa kuwwa: Ana amfani da Amsa kuwwa ne domin jan hankalin jama'a, ita amsa kuwwa, karf ne mai kwaroron baki, da ake kerawa daga tama, sai a doke shi da wani karfen dan karami, sai ya amsa kuwwar, sai ko'ina a jiyo, kusa da nesa.
2. Ganga: Ana amfani da ganga, wadda ake kerawa da fatu ko na rago ko na akuya, wadda iyama, take amsa kuwwa, domin jam hankalin talakawa.
3. Wasika: Ana amfani da wasika, a rubuce da ajami, yaren Hausa amma harufan larabci, ko kuma da larabci, a wasu lokutan ma da fillanci.
4. Waqe, ko qasida: Akan yi amfani da waqa ko qasida domin sadarwa ko isar da sako, musamman tsakanin masoya, ko tsakanin maroka da masu hannu da shuni.
Ga misalin masu gambara nan, wadanda sukan yi waka ne su zayyano surorin mutane masu ma'ana da yabo, domin a basu hatsi ko kudi.
Zamani dai ya kore wadannan irin hanyoyi na sadarwa, inda yanzu mutane kan sami sakonninsu ne ta hanyar wayar salula, wayar gida, talabijin, hotuna, yanar gizo, da sauransu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng