Ana Dab da Zabe, Sojoji Sun Bankado Katunan PVC Sama da 1600 a Wani Gida a Legas

Ana Dab da Zabe, Sojoji Sun Bankado Katunan PVC Sama da 1600 a Wani Gida a Legas

  • Sojin Najeriya sun yi nasarar bankadowa tare da kwato wasu kayayyakin aikata laifi da kuma katunan zaben PVC a wani yankin jihar Legas
  • Rahoto ya bayyana cewa, an kuma kama wasu tsagerun da ake zargin suna da hannu a wannan lamari
  • Ya zuwa yanzu, an ce ana ci gaba da bincike don gano tushen lamarin tare da daukar matakin da ya dace

Jihar Legas - Jami’an rundunar sojin Najeriya na 9 Brigade sun bankado wasu katun zaben PVC 1,671 a wani gida da ke Olodi-Apapa da ke birnin Legas.

Daga baya an kama wasu mutane uku a gidan, yayin da babban wanda ake zargin ya tsere.

Hakazalika, an bankado takardun dangwala zabe, adduna da tarin tabar wiwi duk dai a cikin gidan.

An gano wasu kayayyakin aikin zabe a hannun tsagerun Legas
Kayayyakin da aka kwato daga 'yan ta'adda a Legas | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Jairdar Vanguard ta ruwaito cewa, bankado wadannan kayayyakin ya biyo bayan bincike ne da sojojin ke yi a yankin bayan aukuwar wani lamarin ta'addanci.

Kara karanta wannan

Rudani: DSS ta Gargadi 'Yan Najeriya, Ta Ce Akwai Munanan Abubuwan Da Za Su Faru Bayan Zaben Gwamnoni

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda kayayyakin suke da kuma yadda aka kama su

Kwamandan rundunar, Brig. Gen. Isang Akpaumontia ne ya gabatar da tsagerun da kayan da aka kwato a gaban manema labarai a Legas.

Da yawan katunan zaben da aka kwato suna dauke ne da shekarar rajista 2022, yayin da sauran kuwa suke dauke da shekarar rajista; 2011, 2012 da 2021.

Hakazalika, dukkan masu wadannan katuna mutane ne mazauna jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Ana ci gaba da bincike don daukar mataki

Ya zuwa yanzu, rundunar ta ce za ta ci gaba da bincike ne don gano masu hannu a lamarin kafin daga bisani ta dauki matakin da ya dace, This Day ta ruwaito.

Ba wannan ne karon farko da ake kama wasu ‘yan ta’adda dauke da kayan aikin zabe ba a Najeriya.

Kara karanta wannan

Aiki sai mai shi: Gwamnan jam'iyyar APC ya yi rabon guban bera ga al'ummar jiharsa

Kuma wannan kamu ya zo ne daidai lokacin da ake ci gaba da zabuka a Najeriya; musamman na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi.

An gano wasu katunan zabe a otal a jihar Legas

A jihar Legas din har ila yau, an bankado wasu katunan zabe yayin da ake shirin zaben shugaban kasa a Najeriya.

Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, an bankado katunan zaben ne a cikin wani otal da ke birnin na Legas.

Wani bidiyon da muka samo ya nuna yadda aka bankado kayayyakin a ranar zaben shugaban kasa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel