Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar NSIPA Bayan Dakatar da Halima Shehu

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar NSIPA Bayan Dakatar da Halima Shehu

  • Tsohon kodineta na ƙasa na shirin N-Power, Akindele Egubwalo ya zama sabon shugaban hukumar NSIPA na wucin gadi
  • Hakan ya biyo bayan umarnin dakatar da shugabar hukumar, Dakta Halima Shehu da Shugaba Tinubu ya bayar
  • Shugaban ƙasar ya kuma bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike kan ayyukan Halima a lokacin da take riƙe da shugabancin hukumar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da Dakta Halima Shehu daga muƙaminta na shugabar hukumar jindaɗin al'umma ta ƙasa (NSIPA), bisa zargin tafka almundahanar kuɗi.

Kamar yadda kafar yaɗa labarai ta TVC ta ruwaito, shugaban ƙasan ya amince da naɗin Dr Akindele Egbuwalo ya riƙe muƙamin a matsayin na wucin gadi.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rattaɓa hannu kan kasafin kudin 2024 a Aso Villa, bayanai sun fito

Tinubu ya dakatar da Halima Shehu
Shugaba Tinubu ya nada makwafin Halima Shehu Hoto: Bola Ahmed Tinubu/Halima Shehu
Asali: Twitter

Shugaban ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake yiwa Halima Shehu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dakta Akindele Egbuwalo, wanda ya kasance tsohon kodinetan shirin N-Power na ƙasa, an naɗa shi sabon shugaban hukumar nan take.

A ina Halima ta yi aiki kafin NSIPA?

Halima ta kasance babbar mataimakiya ta musamman ga tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema a shekarar 2011.

Ta kuma bayar da gudunmuwa da ƙwarewarta a matsayinta na ma’aikaciyar hukumar tara haraji ta jihar.

A shekarar 2016, Shehu ta faɗaɗa tunaninta ta hanyar karɓar muƙamin wucin gadi a matsayin mai sa ido kan zaɓen shugaban ƙasa a Cape Verde a ƙarƙashin ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka.

Daga baya, daga shekarar 2017 zuwa 2022, ta kawo ƙwarewarta a ma'aikatar agaji ta tarayya.

Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Kasafin Kuɗin 2024

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun yi martani yayin da Shugaba Tinubu ya yi wani abin ban mamaki a bidiyo

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tiinuɓu ya rattaɓa hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2023, a fadar shugaban ƙasa dake Aso Rock Villa, a birnin tarayya Abuja.

Shugaban ƙasan ya rattaɓa hannu a kan kudin kasafin shekarar 2024 ya zama doka a gaban manyan jiga-jigai da ƙusoshin gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel