Izala Ta Yi Bayani kan Karyar da aka Yi wa Kabiru Gombe game da Tinubu
- Kungiyar JIBWIS ta musanta wani sako da ake yaɗawa a Facebook da ke danganta Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe da yabon shugaban ƙasa Bola Tinubu
- Kungiyar ta ce Sheikh Kabiru Gombe bai taɓa faɗin kalaman da ake danganta masa ba, tare da yin alƙawarin ba da kyautar Naira miliyan 1 ga duk wanda ya kawo bidiyon
- JIBWIS ta bayyana cewa ta riga ta kai ƙorafi ga jami'an tsaro domin bincike kan masu ƙirƙira da yaɗa labaran ƙarya, tana mai gargaɗin masu aikata hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Kungiyar Izala ta musanta wani sako da ke yawo a kafafen sada zumunta, musamman Facebook, wanda ya danganta babban sakatarenta, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, da wata magana kan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyar ta bayyana cewa labarin da ke ikirarin Sheikh Kabiru Gombe ya ce bai taɓa ganin ɗan siyasa mai yawan karatun Alƙur'ani kamar Tinubu ba, ƙarya ce da aka ƙirƙira domin yaudarar jama'a.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwar da JIBWIS ta fitar a Facebook, ta ce irin wannan ɗabi'a ta ƙirƙirar labaran bogi babban laifi ne a gaban doka da kuma addini.
Maganar da Izala ta yi
A cikin sanarwar, kungiyar ta jaddada cewa Sheikh Kabiru Gombe bai taɓa furta kalaman da ake yaɗawa ba.
Ta ƙara da cewa idan akwai wani da zai iya kawo sahihiyar murya ko hujjar da ke nuna malamin ya faɗi wannan magana, kungiyar za ta ba shi kyautar Naira miliyan 1.
Sanarwar ta ce:
"Wannan labari ƙarya aka ƙirƙira aka yaɗa, kuma hakan babban laifi ne ga dokokin ƙasa, haka zalika laifi ne a wajen Allah.
"Sheikh Kabiru Gombe bai taɓa faɗan wannan magana ba. Idan kuma akwai wanda zai kawo muryar inda ya faɗi haka, za mu ba shi tukuicin Naira miliyan 1."
An kai ƙorafi ga jami'an tsaro
Kungiyar ta bayyana cewa ta riga ta kai ƙorafi ga jami'an tsaro domin a binciko mutanen da suke ƙirƙira da yaɗa irin waɗannan labaran ƙarya.
Ta ce idan aka gano waɗanda ke da hannu a lamarin, za a gurfanar da su domin su zama izina ga sauran masu irin wannan ɗabi'a.

Source: Facebook
JIBWIS ta kuma bayyana cewa matakin shari'a zai shafi ba kawai waɗanda suka rubuta labaran ba, har da kafafen da suka yaɗa su ba tare da tantance gaskiyarsu ba.
Martanin jama'a kan sanarwar
Sanarwar ta jawo martani daga mabiya da sauran masu amfani da kafafen sada zumunta. Faruq Ardo ya yi addu'ar Allah ya kare Sheikh Kabiru Gombe tare da ƙara masa lafiya da albarka.
Nasir Ashir ya ce ya kamata kungiyar ta fi mayar da hankali wajen ɗaukar matakin shari'a kan wanda ya fara yaɗa labarin maimakon bayar da kyautar Naira miliyan 1.
Shi ma Abdulrahman Muhammad ya ce zai fi dacewa a gano kafafen da suka yaɗa labarin sannan a hukunta su bisa doka.
Najib A. Usman kuwa ya ce tun farko ya fahimci cewa labarin ba gaskiya ba ne saboda bai dace da halayen Sheikh Kabiru Gombe ba.
Tinubu ya yi ta'aziyyar malami
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma limami, Imam Tijani Olubodun Shehu Gbajabiamila.

Kara karanta wannan
An samu bidiyon babban mai ɗaukar bidiyon Boko Haram da sojoji suka kashe a Borno
Tinubu ya ce marigayin ya kasance jagora mai hikima da kishin addini, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa Musulunci.
Shugaban kasar ya kara da cewa marigayin ya shafe lokaci yana koyar da Alƙur'ani da inganta zaman lafiya da kyawawan ɗabi'u a tsakanin al'umma.
Asali: Legit.ng

