Yarinya Ƴar Shekara 4 Ta Faɗa Rijiya a Kano, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wata yarinya Amina Garba yar shekara hudu da ta fada rijiya
- Saminu Abdullahi, Mai magana da yawun hukumar ne yace wani Alkasim Ibrahim ne ya kira su a waya ya sanar da su faruwar lamarin
- Abdullahi ya ce tawagarsu sun isa wurin cikin gaggawa amma suka ciro yarinyar a sume sannan daga baya jami'an lafiya suka tabbatar ta rasu
Kano - Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wata yarinya yar shekara hudu, Amina Garba, bayan ta fada rijiya a Kofar Waika, da ke kallon Masallacin Karmawi, a karamar hukumar Ungoggo a jihar.
Mai magana da yawun hukumar, Saminu Abdullahi, ya ce hukumar ta Kofar Nassarawa ta samu kiran neman dauki misalin karfe 2.05 na ranar Litinin daga wani Alkasim Ibrahim, The Punch ta rahoto.
Ya ce bayan tawagarsu ta isa wurin, ta gano cewa karamar yarinyar ta fada cikin rijiyar sakamakon tsautsayi.
"Hukumar mu ta samu kiran neman daukin gaggawa misalin karfe 2.05 daga wani Alkasim Ibrahim cewa wata yarinya ta fada cikin rijiya," in ji shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aminiya ta rahoto cewa Abdullahi ya yi bayanin cewa nan take tawagarsu suka garzaya zuwa wurin suka yi nasarar ciro gawar yarinyar wacce daga bisani jami'an lafiya suka tabbatar ta rasu.
Ya ce an mika gawar Amina ga Dagajin Kofar Waika, Alhaji Isma'ila Yusuf, domin daukan matakan da suka dace.
"An ceto wacce abin ya faru da ita a sume kuma daga bisani aka tabbatar ta rasu. An mika gawarta ga dagajin Kofar Waika, Alhaji Ismai'ila Yusuf," ya kara da cewa.
Yaro dan shekara bakwai ya mutu cikin rijiya a Kano
A wani rahoton, Hukumar kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce wani yaro dan shekara bakwai, Umar Ado ya mutu a cikin rijiya a Unguwa Uku by Yarabawa Street a karamar hukumar Tarauni na jihar.
Sanarwar ta fito ne daga bakin mai magana da yawun hukumar, Alhaji Saidu Mohammed a ranar Laraban wannan makon kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Mohammed ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma a lokacin da marigayin ya tafi rijiyar domin ya diba ruwa.
Asali: Legit.ng