Wani mutum ya mutu yayin da ya ke zina da wata budurwa a otel

Wani mutum ya mutu yayin da ya ke zina da wata budurwa a otel

Wani mutum da ba a gano ko waye ba mai matsakaicin shekaru ya mutu a dakin otal, jim kadan bayan shigarsa da wata mata wacce ake zargin budurwarsa ce.

Mamacin, kamar yadda majiyoyi suka ruwaito, ya shiga dakin otal ne tare da budurwar. Bayan mintoci kadan kuwa ya fara ihu tare da dafe kirjinsa wanda har ya jawo hankalin manajan otal din, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, SP Haruna Mohammed ya ce a ranar 30 ga watan Janairu 2020 lamarin ya faru. Wajen karfe 7:45 na yamma ne manajan otal din Jubilee da ke Onitsha ya kai rahoton ga 'yan sandan yankin.

Yayin nuna jarumta: Wani mutum ya mutu a dakin otal da budurwa
Yayin nuna jarumta: Wani mutum ya mutu a dakin otal da budurwa
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Maciji ya kashe wani mai wasa da macizai yayin da ya ke nuna bajintarsa (Bidiyo)

Ya sanar da su cewa wani mutum mai matsakaicin shekaru ya mutu a dakin otal bayan minti talatin da ya shiga tare da wata budurwa.

Kamar yadda manajan ya ce, an hanzarta kai shi asibiti don samun taimakon gaggawa na likita amma sai aka tabbatar da ya rasu.

Ya kara da cewa, jami'an 'yan sandan yankin sun kai ziyara inda abin ya faru tare da daukar hotunan wanda ya rasun.

"Babu alamar tashin hankali ko wani cin zarafi a tare da gawar. An adana gawar a asibitin Boromeo don likitoci su binciki abinda ya yi sanadin mutuwarsa," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel