Tashin Hankali: An Kai wa Fulani Hari Suna tsakiyar Kiwo a Filato, An Rasa Rayuka

Tashin Hankali: An Kai wa Fulani Hari Suna tsakiyar Kiwo a Filato, An Rasa Rayuka

  • An kashe makiyaya uku tare da jikkata wasu biyu bayan wasu dauke da makamai sun kai musu hari yayin da suke kiwon shanu a Riyom
  • MACBAN ta zargi wasu matasa Berom da kai harin, amma kungiyar matasan Berom ta musanta zargin tare da gabatar da nata bayanin
  • Bangarorin biyu sun bukaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike domin gano gaskiya tare da hukunta duk wadanda ke da hannu a harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Filato - Akalla makiyaya uku sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka jikkata bayan wasu dauke da makamai sun kai musu hari a kusa da kauyen Tanjol da ke karamar hukumar Riyom a jihar Plateau.

Wani shugaban matasa a Mahanga, Abdullahi Ibrahim Yusuf, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce makiyayan na kiwon shanunsu ne lokacin da aka kai musu hari.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An cafke wasu yan ƙasashen waje kan zargin hannu a matsalar tsaron Najeriya

'Yan ta'adda sun kashe Fulani Makiyaya da ke kiwo a Filato.
Wasu Fulani da suka rasa muhallansu suna kokarin hada bukkar da za su zauna a sansanin Faladie. Hoto: MICHELE CATTANI/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

An kashe Fulani makiyaya a Filato

Bayan sun kashe makiyayan uku, Abdullahi ya ce 'yan ta'addar sun kuma kashe sa guda daya tare da jikkata wata saniya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya bayyana sunayen wadanda suka mutu da Abdurrazak Abdullahi mai shekaru 22, Husaini Idris mai shekaru 23 da Yusuf Tukur mai shekaru 19.

A cewarsa, Ayuba Adam da Sadi Adamu ne suka samu raunuka a harin kuma an garzaya da su asibiti don ba su kulawa.

MACBAN ta yi Allah wadai da harin

Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN reshen jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa ba tare da wata tsokana aka kai shi ba.

Ya ce bayanan da kungiyar ta samu sun nuna cewa makiyayan na kiwon shanunsu ne lokacin da aka kai musu hari.

Babayo ya zargi wasu daga cikin kabilar Berom da hannu a harin. Sai dai ya bukaci makiyaya su kwantar da hankalinsu tare da kauce wa daukar doka a hannunsu.

Kara karanta wannan

Masanin da ya yi tsayuwar daka yana kare Musulunci a Amurka ya rasu

Haka kuma ya bukaci hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda suka aikata harin tare da gurfanar da su a gaban shari’a.

Kungiyar matasan Berom ta musanta kashe Fulani makiyaya a Filato.
Taswirar jihar Filato inda aka kashe Fulani Makiyaya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kungiyar matasan Berom ta musanta zargin

Kungiyar matasan Berom ta BYM, karkashin jagorancin Barr. Dalyop Solomon Mwantiri, ta yi watsi da zargin da MACBAN ta yi.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran kungiyar, Rwang Tengwong, ya fitar, ya ce zargin ba gaskiya ba ne, yana mai cewa wata hanya ce ta karkatar da hankalin jama'a daga abin da ya faru, in ji rahoton Daily Post.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa mutanen da aka ce an kashe sun kasance cikin wadanda suka kai hari kan al'ummar Jol, amma jami’an tsaro na sa-kai sun dakile harin.

BYM ta kuma yi zargin cewa yayin harin, wani mazaunin yankin mai suna Thomas Damang mai shekaru 48 ya rasa ransa, yayin da wasu mutum uku suka samu raunuka.

An kashe shugaban Fulani makiyaya

A wani labari, mun ruwaito cewa, an kashe shugaban kungiyar Miyetti Allah ta MACBAN a jihar Benue, Ardo Muhammad, tare da wani mutum Yakubu Isah a Otukpo.

Kara karanta wannan

Kebbi: Yan bindiga sun bindige babban darakta, sun sace matarsa da malamar makaranta

An kai harin ne bayan shugaban MACBAN ya halarci taron zaman lafiya da aka shirya tsakanin al’umma da makiyaya a Ohinmini.

Kisan ya jawo tashin hankali a yankunan Otukpo da Ohinmini, yayin da ‘yan sanda suka fara bincike don gano wadanda suka kai harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com