Kaduna: Mutane Sun Taso da Karfinsu, Sun Fara Shirin Kafa Sabuwar Karamar Hukuma
- Al'ummomin Rigasa da Afaka a Kaduna sun fara matakan neman ƙirƙirar ƙaramar hukuma a jihar da ke Arewacin Najeriya
- Kwamitin da ke jagorantar wannan yunƙuri ya miƙa buƙatar ga ƙaramar hukumar Igabi da Majalisar Dokokin Kaduna
- Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa sabuwar ƙaramar hukumar za ta inganta gudanar da mulki, bunƙasa ci gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Rigasa, Kaduna - Masu ruwa da tsaki daga al'ummomin Rigasa da Afaka a Kaduna sun fara neman ƙirƙirar ƙaramar hukuma.
Mutanen sun shirya aiwatar da matakan neman ƙirƙirar sabuwar ƙaramar hukumar Rigasa, tare da tsara Sabon Afaka a matsayin hedikwatarta.

Source: Original
An miƙa wannan buƙata ga ƙaramar hukumar Igabi ta hannun Kwamitin Tsaye da Na Dattawa da ke jagorantar yunƙurin ƙirƙirar sabuwar ƙaramar hukumar daga cikin Igabi, cewar Tribune.
An kafa kwamitin ƙirƙirar ƙaramar hukuma
Jabir Khamis Rigasa ne ke jagorantar kwamitin, yayin da Salisu Sulaiman Afaka ke matsayin sakatare. Alhaji Mu'azu Abubakar Ruma, Tafidan Afaka, shi ne shugaban kwamitin.
Haka kuma, Alhaji Ja'afar Dan Zaria Rigasa na matsayin mataimakin shugaban kwamitin.
Tawagar ta haɗa da 'yan siyasa, shugabannin al'umma, na addini da wakilan ƙungiyoyi domin tabbatar da cimma burinau.
Da farko tawagar ta gabatar da buƙatar ga shugaban ƙaramar hukumar Igabi, Sani Abdul Zangon Aya, kafin ya jagorance su zuwa Majalisar Dokokin Kaduna.
A majalisar, an miƙa buƙatar ga Kakakin Majalisa, Yusuf Dahiru Liman, wanda Honorabul Salisu Bala, mai wakiltar mazaɓar Igabi ta Gabas, ya wakilta.

Source: Facebook
Yankunan da 'karamar hukumar' za ta kunsa
An bayyana cewa sabuwar ƙaramar hukumar za ta haɗa da dukkan al'ummomin da ke ƙarƙashin gundumomin Rigasa da Afaka.
An ce buƙatar ta yi daidai da sashe na 8(3) na kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare: Kotu ta kwace kadarori 48 na Malami a Abuja, Kano da wasu jihohi
Masu neman ƙirƙirar ƙaramar hukumar sun roƙi ƙaramar hukumar Igabi ta goyi bayan wannan shiri, suna cewa hakan zai inganta shugabanci, bunƙasa tattalin arziki da ci gaba.
Sun kuma bayyana cewa sabuwar ƙaramar hukumar za ta inganta isar da ayyukan gwamnati, ta haɓaka ci gaba, tare da biyan bukatun mazauna Rigasa da Afaka yadda ya kamata.
Kwamitin ya ce ya haɗa dukkan takardun da kundin tsarin mulki ya tanada domin ƙirƙirar sabuwar ƙaramar hukuma, tare da nuna fatan hukumomin da abin ya shafa za su amince da buƙatar.
Yadda jihohi ke wasa da kuɗin ƙananan hukumomi
An ji cewa kusan shekara biyu bayan hukuncin Kotun Koli, har yanzu jihohi da dama na ci gaba da sarrafa kudin kananan hukumomi ta asusun hadin gwiwa.
Rahotanni sun nuna an ware wa kananan hukumomi Naira tiriliyan 10.48 tsakanin Yulin 2024 zuwa Yunin 2026, wanda kuma kudin bai shiga hannunsu ba.
NULGE ta ce har yanzu gwamnatin tarayya ba ta fara tura kudin da ake raba wa wa daga FAAC kai tsaye zuwa asusun kananan hukumomi ba.
Asali: Legit.ng
