Nigeria ta fi kowace kasa a Afrika bunkasar tattalin arziki - Rahoton Forbes

Nigeria ta fi kowace kasa a Afrika bunkasar tattalin arziki - Rahoton Forbes

- Babbar cibiyar bincike ta Forbes Africa, ta bayyana Nigeria a matsayin kasar da ta zarce sauran kasashen Afrika a fannin tattalin arziki a 2018

- Tattalin arzikin kasar Nigeria ya zarta na sauran kasashen Afrika da dala biliyan 172, yayin da kasar Afrika ta Kudu ke biye da ita da dala biliyan 166.735

Wata babbar cibiyar bincike da kuma fitar da rahoto kan muhimman abubuwa da suka shafi rayuwar kasashe, Forbes Africa, ta bayyana Nigeria a matsayin kasar da ta zamo zakaran gwajin dafi bayan da ta zarce sauran kasashen Afrika a fannin tattalin arzikin kasa a wannan shekarar ta 2018.

A baya bayan nan ne gwamnatin tarayya da sauran gwamnatocin kasar suka samu akalla zambar miliyan 7 (N7tn) a cikin watanni 11, kamar dai yadda rahoton Forbes ya bayyana.

Tattalin arzikin kasar Nigeria ya zarta na sauran kasashen Afrika da dala biliyan 172, yayin da kasar Afrika ta Kudu ke biye da ita da dala biliyan 166.735.

Nigeria ta fi kowace kasa a Afrika bunkasar tattalin arziki - Rahoton Forbes
Nigeria ta fi kowace kasa a Afrika bunkasar tattalin arziki - Rahoton Forbes
Asali: Instagram

KARANTA WANNAN: Tonon Silili: WAEC za ta bayyana sakamakon jarabawar wani dan takarar gwamna

Haka zalika, a jerin sunayen kasashe da kuma matsayin tattalin arzikinsu na wannan shekarar, kasar Masar ce ta zo ta uku da dala biliyan 78, kasar Alkgeria ta zo ta hudu da dala biliyan 66, yayin da Libiya ta zo ta biyar da dala biliyan 65.

Kasar Botswana ce ta shida da dala biliyan 22.675, sai kasar da ke makwaftaka da Nigeria ta bangaren Yamma wato Ghana ta zo ta bakwai da dala biliyan 20.458, sai Morroco ke binta da dala biliyan 18, kasar Ivory Coast ce ta tara da dala biliyan 11, yayin da kasar Madagascar ta zo ta goma da dala biliyan 6.766.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel