“N1,000 Na Biya Kan Kowace Litar Mai Daya”: Oshiomhole Ya Koka a Bidiyo

“N1,000 Na Biya Kan Kowace Litar Mai Daya”: Oshiomhole Ya Koka a Bidiyo

  • Tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole, ya koka kan siyan litar man fetur a N1,000
  • Oshiomhole ya koka cewa duk da kashe fiye da naira tiriliyan kan tallafin mai, yan Najeriya na biyan fiye da farashin kasuwa
  • A cewar Oshiomhole, N7trn kan tallafin mai bai kunshi kudaden ci gaban fetur ba, yana mai cewa dole a rike wani kan haka

Adams Oshiomhole, tsohon shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, ya koka kan tsadar farashin man fetur a Najeriya.

Da yake jawabi a shirin Politics Today na Channels TV, tsohon gwamnan na jihar Edo, ya koka cewa ya siya litar mai kan N1,000.

Oshiomhole da logon NNPC
“N1,000 Na Biya Kan Kowace Litar Mai Daya”: Oshiomhole Ya Koka a Bidiyo Hoto: NNPC Limited
Asali: Twitter

Akwai mai hannu a karancin man fetur Oshiomhole

Oshiomhole ya ce lamarin ba abun dariya bane, yana mai cewa wani na da hannu a karancin man fetur a kasar nan.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Babu laifin Buhari, Peter Obi ya ce 'yan Najeriya su hankalta, su yiwa Buhari uzuri

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce a yanzu haka, kasar na kashe kimanin naira tiriliyan 7 kan tallafin man fetur amma abun takaici shine cewa yawancin yan Najeriya na biyan fiye da farashin da ya kamata a siyar da mai a kasuwa.

Tsohon Shugaban kungiyar kwadago na kasar ya bayyana cewa duk da naira tiriliyan 7 na tallafin mai, akwai kuma wani kudin haraji na fetur, yana mai jaddada matsayinsa na farko cewa wasu ne ke da hannu a lamarin.

A cewarsa, idan yan Najeriya suna ganin ba sabon abu bane cewa mun saba samun karancin man fetur hatta a mulkin soja har zuwa Shugaba Olusegun Obasanjo, Yar’adua da Jonathan, ana iya cewa karancin mai ya zama dadaddiyar matsala amma wannan baya nufin abun yarda ne.

Tun a Janairu 2022 me kasar ke fama da matsalar karancin man fetur da tsadar farashi a yankuna daban-daban na kasar.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun koma kwana gindin ATM saboda tsananin rashin kudi

Karancin Man fetur da kudi: Rai daya ya salwanta yayin da rikici ya kaure tsakanin jami'an tsaro da yan daba

A wani labari na daban, zanga-zanga kan karancin man fetur da takardun kudi ya zama rikici a garin Ibadan da ke jihar Oyo.

Fada ya kaure tsakanin jami'an tsaro da yan daba lamarin da ya yi sanadiyar rasa ran wani dan sa-kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel