Yadda Gobara Ta Tashi da Dare, Ta Kone Babban Coci Kurmus a Gombe
- Ma'aikatan hukumar kashe gobara ta tarayya sun kashe wutar da ta kama cocin ECWA da ke hanyar Ashaka a jihar Gombe da dare
- Jami'an sun hana wutar yaduwa zuwa sassan ginin coci da kuma gine-ginen da ke kewayen shi, sun kuma ceto dukiyar miliyoyin Naira
- Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne da karfe 8:21 na dare ranar 7 ga Yuli 2026 kuma an fara kokarin kashe ta da gaggawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gombe - Ma'aikatan hukumar kashe gobara ta tarayya (FFS) a jihar Gombe sun yi nasarar kashe gobara da ta kama cocin ECWA da ke kusa da hanyar Ashaka a birnin Gombe, inda suka ceci dukiyar miliyoyin Naira a ranar Talata.

Source: Facebook
Bisa sanarwar da hukumar ta fitar a Facebook, ta ce an fara kai rahoto game da gobarar ne da karfe 8:21 na dare ranar 7 ga Yuli 2026.
Jami'an hukumar sun yi gaggawar zuwa cocin da sauri, inda suka yi aiki kafada da kafada da ma'aikatan hukumar kashe gobara ta jihar Gombe da jami'ar jihar Gombe.
An kashe gobara a coci
Hadin gwiwar da aka yi tsakanin hukumomin ya taimaka wajen kashe gobarar kafin ta yadu zuwa sauran sassan ginin cocin da ma gine-ginen da ke makwabtaka da shi.
Hukumar ta yabi jami'an da suka shiga fagen aiki saboda kwarewa da kuma sadaukarwar da suka nuna wajen kare rayukan al'umma da dukiyarsu.
Kira ga al'ummar jihar Gombe
Hukumar ta yi kira ga al'umma da su dauki matakan kare kai daga gobara da kuma sanar da hukuma nan take idan an ga wuta ta kama wani wuri.
Ta kara jaddada cewa za ta ci gaba da kasancewa a shirye don kare rayuka da dukiya da muhalli a kowane lokaci aka bukaci hakan.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar kashe gobara ta tarayya a Gombe, ASF MB Muazu ne ya sanya hannu a sanarwar da aka fitar a ranar abin da ya faru.
Saƙon jaje da aka turawa coci
Ma'aikatan Halimafactor da ke jihar Gombe sun mika sakon jaje ga jama'ar cocin bisa asarar da suka tafka saboda gobarar.
Sanarwar da suka fitar a Facebook ta ce:
"Muna miƙa saƙon ta'aziyya da alhini ga shugabanni da ɗaukacin mambobin cocin ECWA) da ke kan titin Ashaka a Gombe, sakamakon mummunan gobarar da ta tashi ta lalata ginin cocin tare da ƙone dukiyoyi na miliyoyin Naira."

Source: Facebook
Gobara ta tashi gidan sarki
A wani labarin, mun kawo muku cewa mummunar gobara ta tashi a gidan wani sarki a karamar hukumar Gwagwalada da ke birnin tarayya Abuja.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa mutanen da ke kusa da gidan sarkin sun yi kokain kai masa agaji amma duk da haka wutar ta yi barna.
Biyo bayan kashe gobarar, shugaban karamar hukumar Gwagwalada, Kasim Mohammed Ikwa ya ziyarci gidan sarkin, inda ya roki Allah ya mayar masa da gurbi.
Asali: Legit.ng

