Karin Bayani: Yan ta'addan ISWAP sun gwabza da Mafarauta a Jihar Borno

Karin Bayani: Yan ta'addan ISWAP sun gwabza da Mafarauta a Jihar Borno

  • Rahoto ya bayyana cewa wasu da ake zargin mayakan ISWAP ne sun kai hari kauye a kudancin jihar Borno
  • Wata majiya ta bayyana cewa mafarauta a yankin kauyen sun tarbi yan ta'addan, inda suka yi ɗauki ba daɗi
  • Mamban kungiyar jami'an sa'kai, CJTF, ya bayyana cewa mayakan ISWAP sun ci karfin mafarautan sun shiga cikin ƙauyen

Borno - Wasu yan ta'adda da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne na can sun farmaki wani kauye a kudancin Jihar Borno, kamar yadda Dailytrust ta rahoto.

Yan ta'addan sun farmaki kauyen Shallangba wanda ke kusa da Debiro a karamar hukumar Hawul, jihar Borno.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa mafarauta yan sa kai sun tarbi yan ta'addan, kuma sun fafata da juna yayin harin.

Jihar Borno
Yanzu-Yanzu: Yan ta'adda na can sun buɗewa mutane wuta a wani gari a jihar Borno Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar wata majiya, yan ta'addan sun kai hari ƙauyen a kan motoci, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi yayin da mutanen kauyen suke kokarin tserewa zuwa cikin jeji.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Kashe Fitaccen 'Dan Kasuwan Najeriya a Afirka ta Kudu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani mamban tawagar jami'an tsaron sa kai (CJTF) yace yan ta'addan sun fi karfin mafarautan, yanzu haka suna cikin ƙauyen.

A ranar Lahadi da maraice, wasu yan ta'adda suka kai hari ƙauyukan Debiro, wanda ya haɗa iyaka da kananan hukumomin Biu da Hawul na jihar Borno.

A kwanakin bayan nan dai, yan ta'addan dun matsa da kai hare-hare jihar Borno, inda a wani harin suke sace matafiya.

A wani labarin na daban kuma Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana abinda Buhari ke yi domin kawo karshen kalubalen tsaro a faɗin Najeriya

A kullum shugaba Buhari sai ya yi maganar mutanen da ake kashewa tare da yi musu addu'a, inji fadar shugaban kasa.

Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, yace shugaba Buhari yana damuwa fiye da tunani kan halin rashin tsaro da ake ciki.

Kara karanta wannan

Bidiyon matashi na tura wa 'yan NEPA karnuka yayin da suka zo yanke wuta

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel