“Ba Zai Gwada Shi Da Sarakunan Arewa Ba”: Oluwo Na Iwo Ya Caccaki Obasanjo Kan Sarakuanan Oyo

“Ba Zai Gwada Shi Da Sarakunan Arewa Ba”: Oluwo Na Iwo Ya Caccaki Obasanjo Kan Sarakuanan Oyo

  • Oluwo na Iwo ya bayyana abun da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi wa sarakuna a jihar Oyo a matsayin wulakanta masarautun gargajiya na Yarbawa
  • Oba Abdulrasheed Akanbi, Telu I, a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana cewa Obasanjo ba zai iya gwada hakan a kan sarakunan arewa ba
  • Basaraken ya ce ya kamata Obasanjo ya nuna girmamawa wajen mu’amala da sarakunan gargajiya, cewa mutuntaw abu ne da ya kamata ba wai a nema ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

A ranar Asabar, 16 ga watan Satumba, Oluwo na Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya yi Allah wadai da abun da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi wa wasu sarakunan gargajiya a jihar Oyo.

Oluwo na Iwo ya yi wa Obasanjo wankin babban bargo
“Ba Zai Gwada Shi Da Sarakunan Arewa Ba”: Oluwo Na Iwo Ya Caccaki Obasanjo Kan Sarakuanan Oyo Hoto: emperortelu1
Asali: Facebook

Basaraken ya nuna bacin ransa ga Obasanjo kan umurtan sarakunan gargajiya a jihar Oyo da su tashi su gaishe da shi da Gwamna Seyi Makinde, a wajen kaddamar da aiki a Iseyin, jihar Oyo, cewa hakan tamkar wulakanta kujerun sarautun gargajiya na Yarabawa ne.

Kara karanta wannan

Obasanjo Na Gab Da Rasa Sarautarsa, An Ba Shi Wa’adi Ya Bai Wa Sarakunan Oyo Hakuri

Da yake martani, Oba Akanbi, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren labaransa, Alli Ibrahim, kuma ya yada a shafinsa na Instagram, ya yi Allah wadai da abun da tsohon shugaban kasar ya yi sannan ya nemi wasikar ba da hakuri daga bangaren shi.

Da yake jaddada cewar ba za a iya daukar sarakunan Yarbawa kamar jami'an tsaro da ake bai wa umurni ba, Oluwo ya ga laifin sarakunan da suka bi umurnin Obasanjo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Basaraken ya ce:

"Abun da tsohon janar din ya yi abun Allah wadai ne. Yana bukatar ya tabbatar da kansa a matsayin Bayaraben asali da wasikar ban hakuri. Sarakuna ba yara bane. Mu iyaye ne. Ba zai taba gwada hakan a kan sarakunan arewa ba."

Obasanjo na gab da rasa sarautarsa, an ba shi wa’adi ya bai wa sarakunan Oyo hakuri

Kara karanta wannan

Shugabannin Yarabawa sun yi taro a Legas, sun aikawa Bola Tinubu Sako zuwa Abuja

A halin da ake ciki, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa majalisar Yarbawa ta duniya ta bai wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wa'adin kwana uku ya bai wa sarakunan Oyo da suka halarci bikin haddamar da hanyar Oyo-Iseyin a ranar Juma'a, 15 ga watan Satumba hakuri.

Obasanjo ya sha suka a shafukan midiya bayan an gano shi a cikin wani bidiyo da ya yadu yana cin mutuncin sarakuna saboda basu mike tsaye ba a lokacin da tsohon shugaban kasar ya halarci wani taro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel