Yakin Rasha Da Ukraine Na Iya Tsananta Talauci a Najeriya, Oxfam Ta Yi Gargadi

Yakin Rasha Da Ukraine Na Iya Tsananta Talauci a Najeriya, Oxfam Ta Yi Gargadi

  • Wata kungiya mai yaki da talauci, Oxfam ta nuna damuwar ta akan fadan Ukraine da Rasha inda ta ce zai iya daga farashin kayan abinci a duniya
  • A ranar Laraba, darektan Oxfam na Najeriya, Dr Vincent Ahonsi ya bayyana hakan a Abuja inda ya ce yanzu haka yunwar ta fara yaduwa
  • A cewarsa, Ukraine da Rasha suna taka babbar rawa wurin harkar samar da kayan abinci a kasuwannin duniya wanda hakan babban kalubale ne

Abuja - Wata kungiyar da ta ke yaki akan talauci, Oxfam ta bayyana damuwa dangane da yadda fadan kasar Ukraine da Rasha a cikin makwanni kadan zai iya janyo tashin farashin kayan abinci a duniya. Kamar yadda ta yi kiyasi, farashin zai iya karuwa da kaso 20 cikin 100.

Kara karanta wannan

Dinbin mutane za su rasa aikin yi yayin da Naira ta kara durkushewa kasa a kasuwar canji

Darektan kungiyar Oxfam Na Najeriya, Dr. Vincent Ahonsi, ya sanar da hakan a ranar Laraba a garin Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Yakin Rasha Da Ukraine Na Iya Tsananta Talauci a Najeriya, Oxfam Ta Yi Gargadi.
Oxfam ta yi gargadin cewa yakin Rasha da Ukraine zai iya kara talauci a Najeriya. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ahonsi ya kada baki ya ce wannan fadan ya riga ya janyo fatara da yunwa a kasashen duniya wanda hakan zai iya janyo karancin kayan abinci.

Ukraine da Rasha suna cikin kasashen da ke safarar kayan abinci a duniya

A cewarsa, Ukraine da Rasha suna taka rawa wurin sayar da kayan abinci a kasuwannin duniya.

Kamar yadda ya shaida bisa ruwayar Daily Trust:

“Rasha tana cikin kasashe na sama-sama masu safarar alkama, kuma tana samar da kaso 16% na alkama a kasuwar duniya, yayin da Ukraine ce kasa ta uku mai safarar kusan kaso 10% na alkama a kasuwar duniya.
“Dangane da kasashen da za su shiga yunwa, Ukraine da Rasha zasu taka babbar rawa saboda tasirin su na safarar alkama a duniya.”

Kara karanta wannan

Zaben 2023: 'Yan Najeriya ke son na tsaya takara, ba wai son raina bane, inji Atiku

Ya ci gaba da cewa har tsadar kayan abinci ma zai karu saboda karancin shi.

Kamar yadda ya shaida:

“Kasashen da samun su ba ya da yawa, ciki har da Najeriya ba za su iya jure siyan biredi ba, wanda ake amfani da alkama wurin yin shi a yankuna da dama na kasar.”

Ahonsi ya ce UN ta kiyasta karuwar farashin kayan abinci a kasashen yankin Saharan Afirka

Ya ce fadan zai iya kawo cikas wurin kawo alkamar wanda hakan zai daga farashin ta.

Ya ci gaba da cewa majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewa farashin kayan abinci zai karu a yankin Saharar Afirka da kaso 30 zuwa 40 akan sauran yankunan duniya.

A cewarsa, cikin kankanin lokaci gwamnati zata samar da gaba tsakanin abubuwan da mutane za su iya siya da kuma wadanda ba za su iya siya ba. Sai kuma gwamnatin ta tallafa wa wadanda suke fama da yunwa sakamakon tashin farashin kayan abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel