Dalilin da Ya Sa Mai Ya Sauka a Duniya amma Dangote Bai Karya Kudin Fetur ba
- Jama’a suna mamakin yadda kudin litar man fetur ya ki yin kasa duk da an samu matukar canji a kasuwar duniya
- Matatar Dangote ta yi wa al’umma bayanin abin da ya sa farashin fetur ba zai iya sauka kasa sosai a lokaci guda ba
- Dangote ya ce yana sayen miliyoyin gangunan danyen mai a tsohon farashi don haka ba zai biyewa farashin kasuwar yau ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Lagos - Matatar Dangote ta yi magana game da yadda farashin fetur a Najeriya ya ki sauka sosai duk kudin danyen mai ya yi sauki.
Matatar man ta sanar da cewa ba daga lokaci daya da rage farashin danyen mai ba ne kuma lita za ta sauka a gidajen man da ke Najeriya.

Source: Getty Images
Meyasa Dangote bai karya kudin fetur ba?
Wani rahoto a Business Insider Africa ya nuna Dangote ya bada uzuri da cewa idan ya sayo mai, a kan shafe makonni hudu ba a tace shi ba.
A irin haka ne matatar Dangote ta shigo da ganguna miliyan 40.4 na danyen mai da nufin a tace, an yi hakan ne a Mayu da Yunin 2026.
Sai dai danyen mai ya rage tsada da 24% tsakanin watannin Mayu da Yuni, said ai wannan bai sa mutane a Najeriya suna sayen lita da tsada.
Matatar ta ce mutanen Najeriya za su saye kaya da sauki idan farashin danyen mai ya cigaba da tsayawa yadda yake a haka a kasuwar duniya.
An bukaci matatar Dangote ta rage kudi
Nairametrics ta ce wani jami’in kamfanin Dangote ya fitar da wannan bayani a wata sanarwa da aka fitar domin yi wa jama’a karin haske.
Gwamnatin tarayya da sauran jama’a sun yi ta kira ga Dangote ya sauke kudin fetur sakamakon lafawar da abubuwa suka yi bayan rikicin Iran.

Source: Getty Images
Daga karshen Mayu zuwa yanzu, katafariyar matatar ta rage kudin litar fetur da N200, kuma an rage N300 a farashin kowane lita na dizil.
An samu ragin N520 wajen sayen man jirgin sama sakamakon saukin da matatar ta yi daga lokacin.
Sanarwar ta ce wadannan ragi da aka rika yi sun nuna yadda aka damu da abokan hulda tare da kokarin ganin matatar ta tsaya da kafafunta.
Karin bayani daga sanarwar matatar Dangote
Mafi muhimmancin sanarwar da aka yi shi ne fahimtar da jama’a farashin mai a matatar ba zai rika dacewa da kudin kaya a kasuwar duniya ba.
Babban dalilin da ya sa haka kuwa, a kan saye danyen mai makonni ko watanni kafin a yi aikin tace shi lokacin fetur yana a tsohon farashi.
Saboda ganga ta sake kudi a lokaci guda, hakan ba zai sa matatar da biyewa kasuwar duniya ba..
Lokacin da Dangote ya kara kudin fetur
A farkon shekara an ji labarin matatar man Dangote ta sanar da ƙara farashin litar man fetur a Najeriya bayan kammala bukukuwan ƙarshen shekara.
Matatar ta ɗaga farashin fetur daga N699 zuwa N799 kan kowace lita. Sakamakon wannan ƙarin, gidajen mai na MRS za su riƙa sayar da lita kan N839.
Kamfanin ya bayyana cewa an yi ƙarin ne domin daidaita kasuwa da kuma tabbatar da dorewar samar da mai bayan ragin da aka yi lokacin Kirismeti.
Asali: Legit.ng

