Jadawalin 2024: Jerin Jami’o’i 20 Mafi Daraja a Nijeriya

Jadawalin 2024: Jerin Jami’o’i 20 Mafi Daraja a Nijeriya

  • Jami'ar Covenant ta sake rike kambunta karo na biyu na jami'a mafi daraja a Nijeriya bayan doke jami'ar Ibadan da jami'ar FUTA
  • Times Higher Education, shafin da ke fitar da kididdigar jami'o'i mafi daraja a duniya ya sanar da hakan a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu
  • Manyan jami'o'i 15 na Nijeriya sun fito ne daga Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jami'ar Covenant ta doke jami'ar Ibadan da jami'ar fasaha ta tarayya, Akure, inda ta zamo jami'a mafi daraja a Najeriya a karo na biyu, bisa ga kididdigar Times Higher Education ta 2024.

Kara karanta wannan

Rai baƙon duniya: Jami'ar rundunar sojojin Najeriya ta yi babban rashi a birnin Abuja

Jerin manyan jami'o'i 20 mafi daraja a Najeriya a 2024
Jami'ar Covenant ta sake rike kambunta karo na biyu na jami'a mafi daraja a Nijeriya. Hoto: University of Ibadan
Asali: Twitter

"Jami'ar Covenant ce mafi daraja" - THE

Binciken da aka yi na baya-bayan nan da aka fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa jami’ar Covenant da ke Ota, jihar Ogun, tana cikin manyan jami’o’i 1,000 a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'ar da ke matsayi na 801 a duniya ta fara yin fice a shekarar 2018 bayan da ta samu lambar yabo ta jami'a mafi daraja a Najeriya, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Jami'ar Ibadan ke bin bayan Covenant a matsayin jami'a ta biyu mafi daraja a kasar, yayin da jami'ar fasaha ta tarayya, Akure ta zo ta uku.

Yadda ake fitar da jadawalin jami'o'in

Rahoton shafin Times Higher Education na yanar gizo ya nuna cewa kididdigar jami'o'in duniya mafi daraja ta ƙunshi jami'o'i 1,904 daga cikin ƙasashe da yankuna 108.

Kara karanta wannan

NFF ta nada 'dan Arewa a matsayin sabon mai horar da tawagar Golden Eaglets ta Nijeriya

Rahoton ya ce ana fitar da jadawalin jami'o'in ne ta hanyar la'akari da abubuwa biyar; koyarwa, yanayin muhalli na bincike, ingancin bincike, masana'antu da yadda duniya ke kallon jami'ar.

Jami'o'in Nijeriya daga Kudu da Arewa

Sauran jami'o'in da suka samu matsayi mafi girma a Najeriya sun hada da jami'ar Ilorin, jami'ar Nijeriya, Nsukka, jami'ar Afe Babalola da jami'ar Benin,

Jami'ar aikin gona ta tarayya, Abeokuta, jami'ar fasaha ta Ladoke Akintola, jami'ar jihar Legas, jami'ar Nnamdi Azikiwe, jami'ar Obafemi Awolowo, da jami'ar Fatakwal.

Daga cikin manyan jami'o'i 15 na Nijeriya, tara suna Kudu maso Yamma, biyu a Kudu maso Gabas, biyu a Kudu maso Kudu, daya a Arewa maso Yamma, daya kuma a Arewa ta Tsakiya.

Duba cikakken jerin a kasa:

  1. Jami'ar Covenant
  2. Jami'ar Ibadan
  3. Jami'ar fasaha ta tarayya, Akure
  4. Jami'ar Legas
  5. Jami'ar Bayero, Kano
  6. Jami'ar Ilorin
  7. Jami'ar Nijeriya
  8. Jami'ar Afe Babalola
  9. Jami'ar Benin
  10. Jami'ar noma, Abeokuta
  11. Jami'ar fasaha ta Ladoke Akintola
  12. Jami’ar jihar Legas
  13. Jami'ar Nnamdi Azikwe
  14. Jami'ar Obafemi Awolowo
  15. Jami'ar Fatakwal
  16. Jami'ar jihar Abia
  17. Jami'ar jihar Akwa Ibom
  18. Jami'ar taraya ta Alex Ekwueme
  19. Jami'ar Babcock
  20. Jami'ar Baze

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke hatsabibin ɗan ta'adda da ya yi ajalin janar din soja da wasu sojoji 3

Wuraren shakatawa 5 a Kaduna

A yayin da ake gudanar da bukukuwan karamar Sallah, Legit Hausa ta tattaro bayani kan wasu wuraren shakatawa biyar da ya kamata mutane su ziyarta a jihar Kaduna.

Mafi kyawun wurin taron jama'a domin nishadi, wasannin yara da kuma bude ido shi ne filin wasanni na Gamji, wanda ke tattare da dukkanin abubuwan debe kewa da ake bukata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel