Rahoto: Jerin manyan Jami’o’i 20 da suka yi fice a Najeriya a shekarar 2021, 4 rak aka samu a Arewa
- Kwanan nan Webomotrics ta fito da jerin jami’o’in da suka fi kowane kyau a 2021
- Legit.ng ta fahimci cewa babu jami’o’in Arewa da yawa a wannan jeri da aka fitar
Webometrics ta fitar da jerin jami’o’in da suka fi kowane kyau a Najeriya a wannan shekara ta 2021. A kan fitar da irin wannan jeri a duk shekara.
Kamar yadda muka samu labari, Webometrics ta saki wannan jeri ne a watan Yulin 2021 kamar yadda ta saba yin bincike a kan makarantun Duniya.
Jami'o'in kudu sun yi gaba
Legit.ng ta samu wannan rahoto da aka fitar, inda ta fahimci cewa jami’o’in kudancin Najeriya ne a kan gaba, musamman na yankin kudu maso yamma.
Jami’ar Ibadan ta zo ta farko a wannan karo, sai jami’ar Covenant ta ke biye da ita. Jami’ar da aka rufe kofar sahu na ukun farko ita ce ta Obafemi Awolowo.
Ko da jami’o’in Ibadan da ta Obafemi Awolowo na gwamnatin tarayya ne, jami’ar Covenant da ke Ota, jihar Ogun, da ta yi fice a yau, mallakar ‘yan kasuwa ce.
Jami’o’in da suka zama na hudu da na biyar a jeringiyar shekarar bana sune; jami’ar Najeriya watau UNN ta Nsukka da jami’ar Legas da ake kira UNILAG.
Mafi yawan wadannan jami’o’i sun fito ne daga garuruwan Yarbawa irinsu Ibadan, Legas, Ogun, Ondo, Oyo, da kuma Ekiti, sune su ka dauke 50% na jami’o’in.
Ina makarantun Arewa suka shiga?
Za a fahimci an samu karancin jami’o’in Arewacin Najeriya a jerin. Jami’o’in Ahmadu Bello, da Bayero da jami’ar fasaha ta Minna kadai suka shiga jerin bana.
Daga yankin na Arewa, jami’ar ‘yan kasuwa daya kadai aka samu a shekara nan, ita ce jami’ar Landmark University da ke garin Omu-Aran a jihar Kwara.
A Kudu maso gabas da kudu maso kudu an samu jami’o'in Fatakwal, ta Kalaba, Benin, Owerri da Uyo.
Ya abin yake?
1. University of Ibadan
2. Covenant University
3. Oba Obafemi Awolowo University
4. University of Nigeria
5. University of Lagos
6. University of Port Harcourt
7. Ahmadu Bello University
8. Federal University of Technology Akure
9. Landmark University
10. Federal University of Technology Minna
11. Bayero University Kano
12. Ladoke Akintola University of Technology
13. University of Calabar
14. University of Benin
15. Adekunle Ajasin University
16. Ekiti State University Ado Ekiti (University of Ado Ekiti)
17. Olabisi Onabanjo University (Ogun State University)
18. University of Uyo
19. Nnamdi Azikiwe University
20. Federal University of Technology Owerri
Auren 'dan shugaban kasa
Ku na da labarin yadda Iphone da Ipad suka zama kayan tukwuici a bikin Zahra Nasiru Bayero da Yusuf Buhari wanda aka daura a garin Bichi a makon da ya wuce.
Jama’a suna ta surutai a kan wayoyi da irin kayan da aka raba wa wadanda suka je walimar bikin.
Asali: Legit.ng