Dangote Ya Doke Amurka, Ya Kai Man Jiragen Sama na sama da N750bn zuwa Turai
- Matatar Dangote ta fitar da tan 466,000 na man jiragen sama zuwa Turai a watan Yunin 2026, wanda darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 757
- Najeriya ta zarce Amurka wajen samar wa Turai man jiragen sama a watan Yuni, 2026 yayin da fitar da wannan man daga Amurka ta ragu sosai
- Rahoton S&P Global Commodity Insights ya nuna cewa Najeriya na ƙara ƙarfafa matsayinta a matsayin cibiyar fitar da tataccen mai zuwa kasuwannin duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Matatar man fetur ta Dangote ta sake kafa tarihi bayan rahotanni sun nuna cewa ta fitar da kimanin tan 466,000 na man jiragen sama zuwa nahiyar Turai a watan Yunin 2026, wanda aka kiyasta darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 757.
Wani bincike da S&P Global Commodity Insights ya bayyana cewa wannan adadi ya sa Najeriya ta zarce Amurka wajen samar da man jiragen sama ga kasuwar Turai a watan Yuni, 2026.

Source: Getty Images
Rahoton da jridar Punch ta wallafa ya ce yawan man jiragen saman da Najeriya ta fitar zuwa Turai ya tashi daga tan 232,000 a watan Mayu zuwa 466,000 a watan Yuni, 2026.
Matatar Dangote ta fitar mai zuwa Turai
Business News Nigeria ta ruwaito cewa wannan shi ne mafi girman adadin da Najeriya ta fitar zuwa Turai tun bayan da ƙasar ta fara fitar da man jiragen sama fiye da yadda take shigo da shi a shekarar 2024, lokacin da matatar Dangote ta fara samar da wannan nau'in mai.
Adadin da aka fitar a watan Yuni 2026 ya kai kusan lita miliyan 582.5, kuma idan aka ƙiyasta farashinsa a kan Naira 1,300 kan kowace lita, darajarsa ta kai kusan Naira biliyan 757.25.
A gefe guda kuma, rahoton ya nuna cewa fitar da man jiragen sama daga Amurka zuwa Turai ta ragu daga tan 818,000 a watan Afrilu zuwa 560,000 a watan Mayu, sannan ta ƙara sauka zuwa 399,000 a watan Yuni, 2026.

Kara karanta wannan
Mutumin da ya sayar da yaron abokinsa a kan N1.3m ya tona yadda suke satar yara a Najeriya
Dalilin bunkusar matatar Dangote
Wani ɗan kasuwar mai ya danganta yawaitar man jiragen sama a kasuwar Turai da ƙarin samarwa daga matatar Dangote da kuma matatun mai na Amurka.

Source: Getty Images
A cewarsa:
"An samu wadatar man jiragen sama saboda matatun cikin gida sun ƙara yawan samarwa domin cin gajiyar hauhawar farashin da aka samu a baya. Amurka da Dangote ma sun tura manyan kayayyaki, sannan ana sake ganin jigilar kaya ta mashigar Suez daga Hadaddiyar Daular Larabawa."
Rahoton ya kuma bayyana cewa farashin man jiragen sama a Turai ya ragu sosai bayan tashin hankali da ya biyo bayan rikicin Gabas ta Tsakiya ya lafa.
Matatar Dangote ta rage farashin mai
A baya mun wallafa cewa Matatar Dangote ta rage farashin litar fetur da take sayar wa 'yan kasuwa da N50, inda ta sauke farashin daga N1,175 zuwa N1,125 domin saukaka wa yan Najeriya.
Matatar ta bayyaba cewa faduwar farashin mai a duniya sakamakon lafawar rikicin Gabas ta Tsakiya ne ya jawo ta sauke farashin manta kuma ana sa ran 'yan kasuwar mai na cikin Najeriya za su sauke farashin litar fetur din.
Baya ga rage farashin da ake ba 'yan kasuwa a rumbunan ajiyar manta, matatar Dangote ta kuma rage farashin samar da fetur ta hanyar tashar ruwa wanda ake sa ran zai kara sama wa jama'a sauki.
Asali: Legit.ng
