Hotunan dan Najeriya da ya garzaya kasar waje ya yi wuff da zukekiyar budurwa sun janyo cece-kuce
- Wani dan Najeriya, mai suna Tare Brisibe, ya je Romania inda ya lalubo mata ya aura
- Ya wallafa hotunan aurensa a Twitter, yana nuna tsananin farin cikinsa
- Mutane da dama sun yi ta yabon tsananin kyawun matarsa
Wani mutum dan Najeriya, mai amfani da suna Tare Brisibe, ya janyo maganganu a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ya wallafa hotunan aurensa da matarsa 'yar kasar Romania.
Ya yi wa hotunan take da "idan ka samu kuma ka damke", ya wallafa hotunansa da matarsa wanda suka sanya takunkumi.
Duk da dai 'yan Najeriya da dama sun yi ta cewa ya yi auren ne don samun damar zama a kasar, babu wata soyayya, wasu kuma suna cewa soyayya ce.
Mutane da dama sun yaba yadda sutturar da ya sanya tayi masa kyau, a kalla ya samu mutane 15,000 da suka yaba da hotunan.
Wata Aquessi Emma cewa tayi: "kalle su, kamar ba za su iya rabuwa ba."
"Anyasi emma kuwa cewa tayi, "ka samu cikakkiyar damar zama dan kasar. Barka."
KU KARANTA: Bani da budurwa saboda mata suna tsoron tsayi na, matashi mai kammala hidimar kasa
KU KARANTA: Babban abun alheri da ya taba samun Najeriya shine PDP, Atiku
A wani labari na daban, wata mata ta haihu a sansanin 'yan bautar kasa na jihar Ekiti, inda ta haifi santaleliyar jaririya, jaridar The Cable ta wallafa.
Matar tana daya daga cikin masu bautar kasa 653 da aka tura jihar Ekiti na shekarar 2020 a halin yanzu. Kamar yadda NAN ta ruwaito, Rose Onoja, Kakakin sansanin ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin.
A cewar Onoja, sai da aka garzaya da matar asibitin cikin sansanin lokacin da ta fara nakuda. "Daga asibitin, an mayar da ita Babban asibitin Emure, inda ta haifi jaririya. Yanzu haka matar da jaririyarta suna cikin koshin lafiya," a cewarta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng