Gwamna Abdulrazaq da Saraki sun yi watsi da junansu a filin Idi

Gwamna Abdulrazaq da Saraki sun yi watsi da junansu a filin Idi

  • Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq da Bukola Saraki sun yi biris da junansu yayin da suka hadu a filin Idi
  • An tattaro cewa wannan ne karo na farko da Saraki ke bikin Sallah a jihar tun bayan da Abdulrazaq ya hau karagar mulki
  • Rahoto ya nuna cewa babu kyakkyawar alaka a tsakanin shugabannin biyu

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara da tsohon shugaban majalisar dattijai, Sanata Abubakar Bukola Saraki, sun share junansu a filin Sallar Idi na Ilorin ranar Talata, 20 ga watan Yuli.

Sun haɗu da sauran manyan mutane wajen gabatar da sallah raka’a biyu domin raya bikin na idi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Kotu ta yankewa wani mutum hukuncin wanke bandaki a Abuja na tsawon kwanaki 60 kan yunkurin damfara

Gwamna Abdulrazaq da Saraki sun yi watsi da junansu a filin Idi
Babu kyakkyawar jituwa tsakanin shugabannin biyu Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Wannan shi ne karo na farko da Saraki zai yi Sallar Idi a Ilorin tun bayan bayyanar Abdulrazaq a matsayin gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Badaru Ya Buƙaci Musulmi Su Yi Addu’a Domin Kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Abdulrazaq da jam’iyyar All Progressive Congress (APC) sun fatattaki Saraki da Peoples Democratic Party (PDP) ta hanyar "juyin juya halin O'toge".

Saraki ya isa Ilorin kwanaki hudu da suka gabata, inda ya karbi bakuncin wasu abokansa da dama.

Mutane da yawa sun yi tsammanin tsohon gwamnan na jihar zai tashi daga Ilorin kamar yadda ya yi a lokacin bikin Eid-el-Fitri da ya gabata domin kaucewa rikici tsakanin magoya bayansa da na Abdulrazaq.

Babu kyakkyawar jituwa a tsakanin shugabannin biyu.

Amma ya ba mutane da yawa mamaki yayin da ya iso filin Sallar Idi da misalin karfe 8:30 tare da wasu hadimansa da tsofaffin masu rike da mukaman siyasa wadanda ke masa biyayya.

Daga cikinsu akwai tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Alhaji Kawu Baraje, da tsohon Shugaban Majalisar Dokoki, Dokta Ali Ahmad.

KU KARANTA KUMA: EFCC ta kama wasu mutane 20 da ake zargi da damfara ta yanar gizo a Katsina

Kara karanta wannan

Babbar Sallah: An shawarci masarautar Kano da wasu masarautu su soke hawan sallah

Jaridar ta kuma tattaro cewa Gwamnan ya iso yan mintuna kadan amma yayi biris da shugaban majalisar dattijan.

Tsohon Babban Alkalin Najeriya, Mai shari’a Moddibo Alfa Belgore, Darakta-Janar na Cibiyar Nazarin Dokoki ta Kasa, Farfesa Abubakar Sulaiman, dan takarar Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Mallam Saliu Mustapha, tsohon babban alkalin kotun musulunci, Justis Salihu Olohuntoyin Mohammed, na daga cikin manyan mutane a filin addu’ar.

Eid-el-Kabir: Gwamna Ya Biya Wa Matafiya 6,000 Kuɗin Jirgin Ƙasa Zuwa Gida Sallah

A wani labarin, mun ji cewa a kalla yan Nigeria 6,000 ne suka shiga jirgin kasa daga jihar Legas zuwa Osogbo kyauta da gwamnatin jihar Osun ta biya wa masu zuwa gida hutun Sallah, Daily Trust ta ruwaito.

Wadanda suka amfana da wannan karamcin sun bayyana farin cikinsu bayan sun isa Osogbo a ranar Lahadi suna ta yabawa gwamnatin.

Gwamnatin jihar ta Osun ta bullo da wannan tsarin ne domin saukakawa matafiya wahalar biyan kudin sufuri musamman a wannan lokacin na shagalin sallah.

Kara karanta wannan

An yi luguden wuta tsakanin 'yan fasa-kwaurin shinkafar waje da jami'an kwastam

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng