Kudin UBEC: Saraki Ya Bukaci AbdulRazaq Ya Biya Shi Tarar N20b da Ban Hakuri

Kudin UBEC: Saraki Ya Bukaci AbdulRazaq Ya Biya Shi Tarar N20b da Ban Hakuri

  • Rigimar da ke tsakanin tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da Gwamnan jihar Kwara ya dauki sabon salo
  • Saraki ya maka gwamnan na APC, Abdulrahman AbdulRazaq, a kotu inda ya bukaci ya bashi hakuri da tarar naira biliyan 20
  • Tun farko tsohon dan majalisar ya bukaci Gwamna Abdulrazaq ya janye ikirarinsa na cewa shi (Saraki) ya wawure kudin UBEC yayin da yake matsayin gwamnan jihar

Wani rahoto daga jaridar The Nation ya nuna cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya nemi tarar naira biliyan 20 daga Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara kan yin kalaman batanci a kansa.

Lauyan tsohon gwamnan na jihar Kwara, Afe Babalola & Co, a wata wasika da ya aikewa Abdulrazaq a ranar 30 ga watan Disamba, ya kuma bukaci ban hakuri tare da janye zargin.

Kara karanta wannan

Dirama, Wani Dan Kasuwa Ya Hargitse a Kotun Musulunci Kaduna, Yace Yana Kaunar Matarsa

Abdulrazaq da Saraki
Kudin UBEC: Saraki Ya Bukaci AbdulRazaq Ya Biya Shi Tarar N20b da Ban Hakuri Hoto: Kwara State Government, Bukola Saraki
Asali: Facebook

Saraki ya maka gwamnan Kwara a kotu, ya bukaci makudan kudade

Lamarin ya danganci zargin karkatar da kudaden hukumar kula da ilimi Firamare ta Kasa (UBEC).

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar The Sun ta nakalto wani bangare na wasikar na cewa:

"Wanda muke karewa ya karyata jawabinka da aka nakalto a sama sannan ya jadadda cewa babu kamshin gaskiya a ciki.
"Wanda muke karewa ya yarda cewa ya kamata ka san cewa a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, ba shine gwamnan jihar Kwara ba, don haka ba zai kasance da hannu a kowani badakalar kudade na jihar Kwara ba.
"Bugu da kari, babu wata hujjar cewa, a matsayin shugaban majalisar dattawa, wanda muke karewa ya dogara da ofishinsa ko matsayinsa wajen kare wani daga bincike ko hukunci.
"Ba a ambata ba cewa wanda muke karewa na da dabi'ar shafawa hukumomi bankin fenti da rashin gabatar da kasafin kudinsu ba yayin da yake matsayin shugaban majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Sabuwar Rigima Ta Balle, An Dakatar da 'Yan Takarar Gwamna a Jihohi Hudu

"Duk da haka, ka zabi yin wannan jawabin kan wanda muke karewa.
"Wanda muke karewa ya bayyana cewa kalamanka sharri ne, ba daidai bane kuma yunkuri ne na tunzura al'umma, musamman masu zabe a jihar Kwara da Najeriya baki daya su juya masa baya."

Kada ku yarda a mayar da ku yan daban siyasa, Tambuwal ga matasa

A wani labari na daban, gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal ya yi kira ga matasan Najeriya a kan kada su yarda a mayar da su yan daban siyasa.

Tambuwal ya bukaci matasan da suka fada ma duk dan siyasar da ya nemi su yi bangan siyasa cewa ya hada su da yaransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel