FADAMA III: Manoman tumatir 100 za su samu tallafin kayan aikin gona a Daura

FADAMA III: Manoman tumatir 100 za su samu tallafin kayan aikin gona a Daura

Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar shirin Fadama III na gwamnatin jihar Katsina, ta ce za ta tallafawa kimanin manoman tumatir 100 da kayan aikin gona a cikin yankuna 10 a Daura don bunkasa nomar tumatir a jihar.

Gwamnatin tarayya ta Najeriya tare da hadin gwiwar shirin Fadama III na gwamnatin jihar Katsina, ta yi alkawarin tallafawa manoman tumatir 100 da kayan aikin gona a Daura.

Alhaji Bashir Zango, wanda shine mai kula da shirin Fadama a jihar, ya sanar wa manema labarai a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu a yayin rarraba kayan aikin ga wasu manoma wadanda suka cancanta a Daura.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa, gwamnati ta ba da wannan tallafin kayan aikin gona ne don bunkasa samar da tumatir a jihar.

FADAMA III: Manoman tumatir 100 za su samu tallafin kayan aikin gona a Daura
Manoma

Alhaji Zango ya ce wadanda suka amfana da tallafin sun fito ne daga kungiyoyi masu noman tumatir wato ‘Tomato Growers Associations’ a cikin yankuna 10 a daura.

KU KARANTA: Hukumar NDLEA ta bankado wiwi na N20m a Jihar Edo

Zango ya ce kayan aiki sun hada da jakar taki guda 300 da kayan kashe kwari 30 da na'urorin samar da ruwa guda 30 da kuma bututun ruwa guda 100 don samar da ruwa a cikin gonaki.

"Mun kuma samar da daruruwan gallu na maganin kwari ga manoma", in ji shi.

A cikin jawabinsa, Alhaji Rabe Bala, shugaban kungiyar manoman tumatir a Daura, ya yaba kokarin da gwamnatin jihar ke yi kan wannan shirin.

Shugaban ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya a kan matakin dakatar da shigowa da tumatir a kasar, inda ya jaddada cewa wannan matakin ya karfafa manoman.

Bala ya yi kira ga matasa da su mayar da hankali ga aikin noma tare da yin la'akari da yin zaman kansu da kuma taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel