An Sake Samun Tangarda a Shari'ar da Ake Zargin Ganduje da Karkatar da Kudaden Jihar Kano
- Kotu ta ɗage shari’ar tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje da wasu mutum bakwai zuwa ranar 14 ga Oktoba, 2026
- Ana tuhumar Ganduje da matarsa da wasu kamfanoni da laifuffukan cin hanci da karkatar da kuɗaɗen jihar Kano
- Kotun mai zama a Kano za ta saurari ƙorafin farko da ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙara ya shigar a zama na gaba a watan Oktoba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - An sake samun tsaiko a shari’ar tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da wasu mutum bakwai kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnatin Kano.
A zamanta na jiya Laraba, Babbar kotun jihar Kano ta ɗage zaman shari'ar Ganduje har zuwa ranar 14 ga Oktoba, 2026.

Source: Twitter
Waɗanda ake tuhuma tare da Abdullahi Ganduje

Kara karanta wannan
A wata 1 kacal, hukumar kwastam ta tara kudin shiga sama da Naira biliyan 100 a tashar TinCan
Daily Trust ta rahoto cewa Ganduje na fuskantar tuhume-tuhume guda 11 tare da matarsa, Hafsat Umar, na cin hanci, haɗa baki, karkatar da kuɗaɗen jama'a da kuma amfani da su ba bisa ka'ida ba.
Sauran waɗanda ake ƙara a shari’ar sun haɗa da Abubakar Bawuro, Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, da kamfanonin Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited da Lasage General Enterprises Limited.
Abin da ya faru a zaman kotun Kano
A zaman kotun na ranar Laraba, lauyan masu gabatar da ƙara watau gwamnatin Kano, Victor Oni, ya sanar da kotun cewa gwamnati ta shirya ci gaba da shari’ar.
Ya nemi izinin kotu domin janye wata takarda da aka gabatar tun ranar 31 ga Maris, 2026, tare da maye gurbinta da sabuwar takarda mai ɗauke da kwanan watan 15 ga Mayu, 2026.
A cewarsa, sabuwar takardar ta mayar da martani ne ga ƙorafin farko da kuma buƙatar dakatar da shari’ar da wanda ake ƙara na shida ya gabatar.

Kara karanta wannan
EFCC za ta gurfanar da shugaban Fulani na Miyetti Allah bayan cafke shi kan $2.5m
Kotu ta ɗage zama zuwa Oktoba
Lauya da ke kare Ganduje da matarsa da ɗansa, Lydia Oluwakemi-Oyewo, ta bayyana cewa ba su da wata adawa kan buƙatar da masu gabatar da ƙara suka yi.
Haka kuma lauyoyin da ke kare sauran waɗanda ake ƙara sun nuna shirinsu na ci gaba da sauraron shari’ar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Sai dai lauyan wanda ake ƙara na shida, Abubakar Ahmad, ya sanar da kotu cewa ya gabatar da ƙorafi na farko tare da hujjoji da bayanan kariya, inda ya buƙaci a ware ranar da za a saurari buƙatarsa.

Source: Getty Images
Bayan sauraron ɓangarorin, Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta amince da janye tsohuwar takardar masu gabatar da ƙara tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 14 ga Oktoba, 2026.
Gwamnatin Kano ta nemi karin lokaci
A baya, kun ji cewa Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta kawo tsaiko a zaman shari'ar tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.
Gwamnatin Kano ta maka Ganduje gaban kotu tare da matarsa Hajiya Hafsat Umar, da wasu mutane shida bisa tuhuma 11.
Gwamnatin ta nemi ƙarin lokaci domin mayar da martani kan korafin neman dakatar da shari’a da waɗanda ake tuhuma suka shigar tun ranar 19 ga Nuwamba, 2025.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
