An Kama Budurwa Da Saurayi Da Ke Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ta Intanet a Abuja

An Kama Budurwa Da Saurayi Da Ke Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ta Intanet a Abuja

- Jami'an hukumar NDLEA sun yi nasarar kama wasu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi

- Cikin wadanda aka kama har da wata budurwa da saurayinta da ke sayar da kwayoyin a Instagram

- An kuma kama wani mutum da ke da babura guda biyar da ake masa amfani da su wurin rabar da miyagun kwayoyi

Hukumar Yaki Da Hana Safarar Miyagun Kwayoyi na Kasa, NDLEA, ta ce ta kama wasu mutane da ake zargi da safararmiyagun kwayoyi a birnin tarayya Abuja, The Cable ta ruwaito.

Femi Babafemi, kakakin NDLEA, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi ya ce an kama su ne sakamakon samamen da hukumar ta yi cikin wannan makon

An Kama Budurwa Da Saurayi Da Ke Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ta Intanet a Abuja
An Kama Budurwa Da Saurayi Da Ke Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ta Intanet a Abuja. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan

Cikin wanda aka kama akwai wata Ese Patrick da ake zargi na siyar da miyagun kwayoyi a dandalin Instagram.

Babafemi ya ce an kama yar shekaru 28 din tare da saurayinta a yayin da suka iso kawo miyagun kwayoyin da jami'an hukumar NDLEA wadanda suka yi basaja suka yi oda ta intanet.

Ya ce hukumar ta kuma tafi gidan Patrick inda ta kwace kilogram 400 na 'ganyen wiwi na Arizona' wacce ta ke amfani da shi wurin sarrafa biskit din 'brownies'.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai 200 a Makarantar Islamiyya a Neja

Har wa yau, an kama wani da ake zargi, Peter Nkejika, a ranar 24 ga watan Mayu bayan an kama mai kai masa sakonni kan babur da wani samfurin ganyen wiwi da ake kira 'Loud' na kimanin N510,000.

Kazalika, an kama wani Dolapo Benjamin, wanda aka ce ya mallaki babura biyar da ake amfani da su wurin kai wa mutane miyagun kwayoyin a gidajensu.

A wani labarin daban, wani matashi ɗan Nigeria mai suna @sarnchos a ranar Talata, 25 ga watan Mayu ya bayyana yadda wani dattijon bahaushe ya riƙe amanan mahaifinsa tsawon shekaru 30.

A wani rubutu da ya yi a baya tun shekarar 2019, ya rubuta kan yadda wani mutum da ya fi shekaru 90 a lokacin ya riƙa kula da gonar mahaifinsa tun a 1992.

@sarnchos ya bayyana cewa tsawon shekaru kimanin 30, dattijon bai taɓa karbar wani albashi ko lada ba sai dai yana ciyar da kansa ne da abin da ya ke noma wa a gonar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164