Yan Bindiga Sun Kai Sabon Farmaki Kauyen Sokoto, Sun Yi Mummunar Barna

Yan Bindiga Sun Kai Sabon Farmaki Kauyen Sokoto, Sun Yi Mummunar Barna

  • Akalla mutum shida ne aka yi garkuwa da su yayin da aka kashe mutum daya a wani sabon farmaki da 'yan bindiga suka kai a wani kauyen Sokoto
  • Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da kai harin inda ta ce maharan sun shiga kauyen Tursa da sanyin safiyar Talata kuma sun yi barna
  • Jihar Sokoto na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar 'yan bindiga da ke masu hare-hare a duk sa'ilin da suka ga dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Sokoto - Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu shida a wani hari da suka kai kauyen Tursa da ke karamar hukumar Rabba a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

An shiga dar-dar yayin da ’yan bindiga suka sace mace mai juna biyu, da wasu mutum 22 a Taraba

An kai harin ne da sanyin safiyar Talata.

Yan bindiga sun kai sabon hari Sokoto
Rundunar 'yan sanda ta ce 'yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyen Sokoto, inda suka kashe mutum daya da sace wasu. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, Ahmed Rufa’i, maharan sun mamaye kauyen inda suka kona wani gida inda mutum daya ya mutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an kona wasu kadarori da suka hada da babura yayin da aka kuma sace wasu dabbobi da ba a tantance adadinsu ba, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin farautar wadanda ake zargi da aikata laifin, ya kuma yi alkawarin bayar da karin bayani idan an samu nasara.

Hare-haren 'yan bindiga a Arewa maso Yamma

Sokoto dai na daya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar ‘yan fashin daji da ke kai hare-hare a duk sa'ilin da suka ga dama.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Sama da 'yan Najeriya 1,000 aka damfara da sunan sama masu aiki a Burtaniya

Sauran jihohin sun hada da Kaduna, Kebbi, Zamfara da Katsina.

A wani bangare na matakan da ake dauka kan ‘yan bindiga a yankin, sojojin Najeriya na kaddamar da hare-hare ta sama tare da kashe wasu ‘yan ta’adda da manyan kwamandojinsu.

‘Yan bindiga sun dade suna addabar wasu jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya, inda suke gudanar da ayyukansu daga sansanoninsu da ke a dazuzzukan yankunan.

A hare-haren da suke kai wa kauyukan, suna kwasar ganima da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Yan bindiga sun mamaye wani kauyen Zamfara, sun kashe mutane da dama

A wani labarin, 'yan bindiga sun kai wasu sabbin hare-hare a garin Zurmi da ke jihar Zamfara, inda suka kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar na kai hare-haren ne biyo bayan kwace shanun sata da sojoji suka yi daga hannun su

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel