Babban sarki a Najeriya ya saki matarsa, ya ce ta zama sarauniya mai 'murabus'

Babban sarki a Najeriya ya saki matarsa, ya ce ta zama sarauniya mai 'murabus'

Sanannen basaraken kasar yarbawa, Oluwo na kasar Iwo, Oba Abdulrasheed Akanbi ya saki matarsa mai suna Chanel Chin. Hakan ya bayyana ne daga wallafar da ya yi a shafinsa na Instagram a ranar 15 ga watan Disamba, 2019.

A takardar da sakataren yada labarai na Sarkin yasa hannu, basaraken ya bukaci jama’a, abokai da makusanta da su kiyaye duk wani kasuwanci ko bukata da aka yi amfani da ofishin sarauniyar.

Kamar yadda Ibraheem ya sanar, auren ya rabu ne saboda ‘dalilian da ba za a iya sasantawa ba’.

“Ana sanar da jama’a ballantana abokai da makusantan Oluwo na kasar Iwo, a kan cewa mai martaba Oba (Dr.) Abdulrosheed Adewale Akanbi, Telu I, cewa Chanel Chin a halin yanzu ta zama tsohuwar sarauniyar mai martaba.

“Wannan labarin ya zama wajibi don gudun bada wani girma da yake da dangantaka da karagar mulkin Oluwo din gareta. A saboda dalilin banbanci wanda ba zai sasantu ba, Chanel Chin ta rabu da Sarkin kuma a halin yanzu ba sarauniyarsa bace.

DUBA WANNAN: Kano: Sarkin Karaye ya sauke manyan hakimai guda 2 a karkashin masarautarsa

A don haka, ake bukatar jama’a da su guji kasuwanci ko wata alfarma daga wajenta da aka dangana da ofishin mai martabar.

“Muna mata fatan alheri a al’amuranta,” in ji takardar.

Basaraken ya bayyana cewa ya fi Sango da Ogun; magabatansa. Ya wallafa hakan ne a shafinsa na Intsagram a kwanakin baya.

A walllafar basaraken, yace dole ne ‘da ya fi ubansa da magabatansa.

“Ina takamar zama ‘da ga Sango da Ogun, amma dole ne in fi Sango da Ogun daukaka. Daukaka bai kamata ta tsaya a kan magabatanmu ba. Wanda ya fi Sango daukaka gashi nan. Ba rashin mutunta magabata bane.

“Idan har ban fi magabatana daukaka ba, ban kyautatawa tarihin da magabatan nawa suka kafa ba!” Yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel