An Tsinci Gawar Wata Mata Mai Yara 2 a Dakinta Bayan Ta Yi Magana da Mijinta

An Tsinci Gawar Wata Mata Mai Yara 2 a Dakinta Bayan Ta Yi Magana da Mijinta

  • Wata ‘yar Najeriya mai suna Joy Nsude, mai ‘ya’ya biyu, namiji da mace a kasar Birtaniya, ta rasu a gidanta da ke Hartlepool.
  • An bayyana cewa Nsude ta rasu ne a ranar 2 ga watan Nuwamba bayan kammala tattauna da mijinta da wasu a wayar tarho
  • Wata yar Najeriya mazauniyar kasar Birtaniya, Ibironke Quadri, ta sanar da rasuwarta, kuma har yanzu ba a san musabbabin mutuwar ta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kasar Birtaniya - Wata ‘yar Najeriya mai suna Joy Nsude da ke zaune a kasar Birtaniya (UK), ta gamu da ajalinta a gidanta da ke Hartlepool jim kadan bayan gama tattaunawa da mijinta da wasu mutanen a wayar tarho.

Kara karanta wannan

Jami'ar Baze ta karrama 'first lady' Maryam Babangida shekaru 14 bayan rasuwarta

Marigayiyar dai uwa ce ga ‘ya’ya biyu, yaro dan shekara 4 da yarinya ‘yar shekara 2, kamar yadda rahoton Vanguard ya nuna.

Joy Nsude
An tsinci gawar matar ne a dakinta, bayan ta yi magana da mijinta a wayar tarho Hoto: Ibironke Khadeejah Quadri
Asali: UGC

Ibironke Khadeejah Quadri, ‘yar Najeriya mazauniyar kasar Birtaniya, ta sanar da rasuwar ta a shafinta na Facebook a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, inda ta kara da cewa har yanzu ba a san dalilin mutuwar ta ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Quadri, Nsude ta kasance dalibar Jami’ar Teesside, Middlesbrough, a fannin 'International Management', kafin rasuwarta a ranar 2 ga watan Nuwamba.

Yadda 'yar Najeriya, Joy Nsude, ta rasu a Birtaniya

Ta rubuta:

“A cikin bakin ciki ne muke sanar da ku rasuwar babbar mamba a kungiyar mu ta 'yan Najeriya da ke karatu a jami'ar Teesside University, Middlesbrough, Birtaniya, mai suna Joy Osunde, daliba ce da ke karantar fannin 'International Management'."

Kara karanta wannan

An garkame babban malamin addini a gidan yari kan zargin damfarar miliyan 305, bayanai sun fito

“Ita mahaifiya ce ga yara biyu, yarinya ‘yar shekara 2 da yaro dan shekara 4."
"Ta rasu ne a gidanta a ranar 2 ga Nuwamba, 2023, a Hartlepool, bayan ta yi magana da mutane da yawa ta wayar tarho ciki har da mijinta."

Ta ci gaba da cewa:

"Shi kuma yana kan hanyarsa ta zuwa aiki a wannan rana mai muni, kuma har yanzu ba a san musabbabin mutuwar ta ba."
"Mai shari’a Nwaru, mijin matar wanda ke cikin dimuwa a halin yanzu, yana neman taimako daga abokai, iyalai, kungiyoyi, cibiyoyi, don ba shi damar shirya jana’izarta.”

Dan Najeriya ya makale a Birtaniya

Wani dan Najeriya ya shiga damuwa bayan matarsa da ke cin amanarsa ta soke bizarsa na Birtaniya, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Wani mai amfani da shafin Twitter, @Wizarab10, wanda ya yada labarin, ya bayyana cewa mutumin ya gano cewa matarsa na cin amanarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel