Mele Kyari: Tsohon Shugaban NNPCL Ya Fada Komar EFCC, an Ji Dalili
- Tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya isa hedkwatar hukumar yaki da cin hanci ta EFCC da ke Abuja
- Akwai yiwuwar Mele Kyari zai sha tambayoyi kan yadda wasu al'amura suka gudana a kamfanin NNPCL lokacin da yake jan ragamarsa
- A baya kotu ta taba bayar da umarnin rufe asusun banki da aka danganta su da Mele Kyari bayan EFCC ta bukaci hakan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya kai kansa hedkwatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa da ta'annati da dukiyar kasa (EFCC) a Abuja.
Mele Kyari ya bayyana a hedkwatar hukumar EFCC ne a ranar Laraba, 10 ga watan Satumban 2025.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa tsohon shugaban na kamfanin NNPCL ya isa hedkwatar hukumar EFCC ne da misalin karfe 2:30 na rana.

Kara karanta wannan
Kotun Amurka ta kama tsohon shugaba a NNPCL da cin hanci, zai sha daurin sama da shekaru 10
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Mele Kyari ya je hannun EFCC?
Majiyoyi sun bayyana cewa Mele Kyari, wanda aka taba saka sunansa a jerin wadanda ake sa ido a kansu, ya je hukumar ne domin amsa tambayoyi.
Zai amsa tambayoyi ne kan yadda aka yi amfani da kudaden da aka ware, domin gyaran matatun mai a kasar nan a lokacin da yake rike da mukamin shugabancin kamfanin NNPCL
"Eh, yana ofishinmu. Za a kai shi inda manyan jami’anmu za su fara yi masa tambayoyi.”
- Wata majiya
Kyari ya taba musanta shiga hannun EFCC
Hakazalika, a baya tsohon shugaban na kamfanin NNPCL ya taba musanta cewa hukumar EFCC ta tsare shi.
Ya bayyana cewa labarin kamunsa ba komai ba ne face karya wadda ake yadawa da nufin bata masa suna a idon al'umma.
A baya dai, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin a rufe wasu asusun asusun banki guda hudu da aka danganta da Mele Kyari, bisa bukatar da hukumar EFCC ta gabatar.

Kara karanta wannan
'Sun fara kamfe a sakaye,' INEC ta fadi yadda 'yan siyasa su ke birkita mata lissafin 2027
Alkalin kotun mai shari’a Emeka Nwite ne ya yanke hukuncin a ranar Talata, 19 ga watan Agustan 2025, bayan lauyan EFCC, Ogechi Ujam, ya shigar da bukatar gaggawa a gabansa.
Hukumar EFCC ta shigar da bukatar ne bisa korafin da Guardians of Democracy and Rule of Law ta mika mata na zargin tsohon shugaban na kamfanin NNPCL da sata.

Source: Facebook
Karanta wasu labaran kan kamfanin NNPCL
- "Ana barazana ga rayuwata," Shugaban NNPCL ya tona masu son raba shi da mukaminsa
- Asiri ya tonu: NNPCL ya gano hannun kungiyoyin kasashen waje a satar man Najeriya
- Shugaban EFCC ya kare kansa kan batun tilastawa Ojulari yin murabus a NNPCL
Kotu ta samu tsohon shugaba a NNPCL da laifi
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kotu a kasar Amurka ta samu tsohon Janar Manaja a kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Paulinus Okoronkwo, da laifi.
Kotun ta samu Paulinus Okoronkwo ne da laifin karbar rashawa ta Dala miliyan 2 daga wani kamfanin man fetur.
Tsohon Janar Manajan na iya fuskantar daurin shekara 10 a gidan gyaran hali kan kowane laifi na halatta kudin haram.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng