Yadda Rikicin Gona Ya Yi Sanadin Kashe Sojoji 17 a Jihar Delta, In Ji Shugaban Al’umma

Yadda Rikicin Gona Ya Yi Sanadin Kashe Sojoji 17 a Jihar Delta, In Ji Shugaban Al’umma

  • Wani shugaban al'umma a garin Okuoma da ke jihar Delta, ya fadi yadda rikicin gona ya yi sanadin kashe sojoji har 17 kwanan nan
  • Olorogun Sleek Oshare, ya bayyana cewa rikicin gona ne ya jawo komai, yana mai ikirarin cewa sojojin sun ɗauki bangaranci a lamarin
  • Oshare ya gargadi mahukunta kan daukar mataki ba tare da yin kwakkwaran bincike ba, yana mai cewa 'ana bugun jaki, an barin taiki'

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Delta - Olorogun Sleek Oshare, wani shugaban al'umma a jihar Delta, ya ce rikicin gona ne ya jawo aka kashe sojoji a jihar.

Akalla sojoji 17 ne aka kashe a garin Okuoma da ke jihar Delta a makon da ya gabata, lamarin da ya jawo tofin Allah-tsine daga al'ummar Najeriya.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dan takarar shugaban kasa na LP ya ziyarci Musulmi an yi buda baki da shi

Abun da ya jawo aka kashe sojoji a Delta
Okoma: Garin da rikicin gona ya zama silar mutuwar sojojin Najeriya. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

A yayin tattaunawa da Channels TV a shirinta na 'siyasa a yau', Oshare ya ce sojojin sun je garin ne domin sasanta rikicin gona tsakanin Okuama da wani kauye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gaskiyar abin da ya faru a Okuoma

Oshare ya ce 'yan Najeriya ne ba su fahimci gaskiyar abin da ya faru ba, da har ake ɗora alhakin kashe sojojin kacokan a kan mutanen garin.

Oshare ya ce:

"Fada a kan gona ne ya jawo duk abin da ya faru. Iyalan wannan gari na rikici da iyalan garin makwabta, kuma an saba yin hakan.
"Sai dai garin Okuoma ya fahimci sojoji na goyon bayan dayan garin. Mu ne aka gogawa kashin kaji saboda ba mu da daurin gindin kowa."

Fadan Okuoma da Okoloba ya shafi sojoji?

Shugaban al'ummar ya koka kan yadda babu wanda ke magana a kan garin Okoloba wanda Okuoma ke rigimar gonar da su.

Kara karanta wannan

Yadda za a bi a maido Dalar Amurka N160 daga N1600 Inji Masanin tattalin arziki

Shugaban al'ummar ya ce:

"Sojoji suna goyon bayan ahalin wadanda ke rigimar da ahalin Okuoma. Ko yanzu aka je garin Okoloba, za a tarar sun tsere, saboda suna tsoron su ma za a kai masu hari.
"Har sai an gudanar da sahihin bincike ne za a gano gaskiyar abin da jawo aka kashe sojojin. Ina da tabbaci daga nan ne za a fara jajanta mana ba wai a dora mana laifi ba."

Gwamnati da sojoji sun dauki mataki?

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an bankawa garin Okuoma wuta biyo bayan kasashe sojojin da aka yi, lamarin da ya jawo asarar dukiya da jikkata mutane.

Sai dai Oshare ya ce:

"Mu yi hattara da wadanda za mu dora wa alhakin wannan lamari. Muna sane da cewa akwai wadanda ke son bata sunan Okuoma a wajen jami'an tsaro."

Tun bayan faruwar lamarin, gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Delta da jami'an tsaro na soji, sun lashi takobin kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Kara karanta wannan

Yaron gida ya kashe uwar dakinsa da katako kwanaki 7 da fara zuwansa aiki a Legas

Majalisar dattawa ta nemi diyyar sojoji

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu da ta biya diyyar sojojin da aka kashe a Delta.

Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin da hukumomin tsaro da su tabbatar sun yi duk mai yiwuwa na kama wadanda suka aikata laifin domin ayi masu hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel