Wani yaro dan shekara 12 ya fada rijiya a Kano

Wani yaro dan shekara 12 ya fada rijiya a Kano

A jiya, Talata ne wani yaro mai shekaru 12, Saifilahi Isa ya fada rijiya a garin Bagadawa da ke karamar hukumar Dawakin Tofa da ke jihar Kano.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar kiyaya gobara na Kano, Alhaji Saidu Muhammad ya shaidawa kamfanin dillancin labarai a ranar Laraba cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 3.08 na yamma.

Ya bayyana cewa mahaifiyar Isa ce ta aike shi rijiya domin ya dibo mata ruwa.

Wani yaro dan shekara 12 ya fada rijiya a Kano
Wani yaro dan shekara 12 ya fada rijiya a Kano
Asali: Twitter

"Mun samu rahoton afkuwar lamarin ne a yammacin Talata daga ofishin mu da ke Dawanau misalin karfe 3.08 na yamma cewar wani yaro ya fada rijiya.

"Nan take muka tura jami'an mu domin su tafi wajen su tai dauki inda suka isa wajen misalin karfe 3.25 na yamma.

"An ciro Isa daga cikin rijiyar a sume kuma aka garzaya da shi zuwa babban asibitin Dawakin Tofa inda likitoci suka tabbatar da cewa ya rasu," a cewar Muhammed.

Ya shawarci iyaye da ke da rijiyoyi a gidajensu su kara tsawon dakalin rijiyoyin kuma su sanya murfi domin kiyaya kananan yara daga afkawa cikin rijiyoyin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: