Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

Yadda matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa ya karbi naira miliyan 2 kuɗin fansa

- An kama wani matashi mai shekara 20 da laifin garkuwa da mahaifinsa a birnin tarayya Abuja

- Matashin wanda ya hada kai da abokan sa suka amshi kudin fansa miliyan 2 ya samu 200,000 a matsayin kason shi

- Hukumar yan sanda ta cafke matashin tare da abokan sa a ranar Laraba 20 ga watan Janairun 2021

Rundunar yan sandan Najeriya, ta cafke wani dan shekara 20, Abubakar Amodu, bisa shirya tawaga don garkuwa da mahaifin sa tare da karbar kudin fansar miliyan biyu, The Nation ta ruwaito.

Amodu na daya daga cikin masu laifi 25 da kakakin rundunar yan sanda, CP Frank Mba, ya kama da laifuka daban daban a Abuja.

Dan shekara 20 ya yi garkuwa, ya karbi kudin fansa naira miliyan 2
Dan shekara 20 ya yi garkuwa, ya karbi kudin fansa naira miliyan 2. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: FG ta yi wa gwamnan Ondo gargadi kan korar makiyaya daga jiharsa

An kama wanda ake zargin, tare da wasu yan tawagar sa, ya ce yana aiki da mahaifinsa suna aikin kiwo a gona.

A cewar sa, baban nasa ya bashi shanu 15 kuma ya bar gidan.

Ya ce ya kulla abota da abokan tawagar tasa, wanda suka shaida masa mahaifin sa mai kudi ne, ya kamata ayi garkuwa da shi a samu kudi.

KU KARANTA: 'Yar shugaban Amurka Trump za ta auri saurayinta da ya girma a Nigeria

Ya amsa hada tawaga da tayi nasarar sace mahaifin nasa kuma ya samu naira 200,000 a cikin kudin.

Kakakin yan sanda, CP Frank Mba ya ce lokaci ya yi da rundunar za ta daina ragawa yan ta'adda.

A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel