'Yan Sanda Sun Cafke Rikakkun Masu Garkuwa da Mutane, An Kwato Kudi da Makamai
- Ƴan sanda sun cafke wani mutumi mai shekaru 60 da wasu biyu bisa zargin satar mutane a Asaba, jihar Delta
- Bayan haka, 'yan sanda sun kwato N4.1m da masu garkuwar suka karɓa a matsayin kudin fansa daga wanda suka sace
- Rundunar ta kara da cewa ta ceci wata mata daga hannun masu garkuwa da mutane, ta kuma kwato bindigar AK-47
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Delta - Rundunar ƴan sanda ta jihar Delta ta ce ta kama wani mutum mai shekaru 60 da wasu biyu bisa zargin yin garkuwa da mutane tare da karɓar kudin fansa.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Abaniwonda Olufemi, ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar rundunar da ke Asaba, babban birnin jihar.

Source: Twitter
An cafke masu garkuwa da mutane
CP Abaniwonda Olufemi ya ce jami’an rundunar sun gano N4.1m daga cikin kudin da aka karɓa daga wanda aka sace, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, bayan samun rahoton garkuwa da mutane biyu a ranar Asaba ranar 3 ga Oktoba, rundunar ta tura jami’an yaki da garkuwa da mutane da laifuffukan yanar gizo domin gudanar da bincike.
Binciken ya kai ga cafke Ndianefo Cypre, mai shekaru 60, wanda aka gano cewa asusun bankinsa ne aka yi amfani da shi wajen karɓar kudin fansa.
An kuma kama wani Onwe Sunday, mai shekaru 49, a Ihiala, Anambra, inda aka samu ₦1.5m a hannunsa, wadanda suka fito daga kudin fansar.
Delta: An kamo sauran masu laifi
Kwamishina Olufemi ya ce bayan karin bincike da kuma tattara amsoshin tambayoyi daga waɗanda aka kama, 'yan sanda sun cafke wani Uzoma Ifeanyi Chukwu a Nnewi, jihar Anambra.
A wurin binciken, ƴan sanda sun gano N2.6m daga hannunsa, wanda ya zama wani ɓangare na kudin fansar da aka karɓa daga wanda aka sace.
Kwamishinan 'yan sanda ya tabbatar da cewa dukkan waɗanda ake zargi suna hannun rundunar yanzu, kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

Source: Original
Ƴan sanda sun ceto matar da aka sace
Hakazalika, kwamishinan ƴan sandan ya ce sun samu rahoton cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari kan wani mutum a Obinomba community, yayin da yake kan babur tare da ’yar uwarsa.
CP Oluemi ya ce masu garkuwar dauke da bindigogi sun sace matashiyar tare da shigar da ita cikin daji.
Ya ce 'yan sanda tare da 'yan sa kai ne suka bi sawun masu garkuwa zuwa cikin daji, inda aka yi musayar wuta da ta kai ga kashe ɗaya daga cikin miyagun.
A cewar Olufemi, an ceto wadda aka sace ba tare da rauni ba, yayin da aka kwato bindigar AK-47, gidan harsashi guda ɗaya, da harsasai 12.
An gano mabuyar masu garkuwa da mutane
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ’yan sanda sun ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kano da Kaduna tsakanin 7 zuwa 9 ga Oktoba, 2025.
Wani matashi da ya tsere daga hannun masu garkuwa ya taimaka wa 'yan sandan na Kano wajen gano maboyarsu a Saya-Saya, karamar hukumar Ikara, Kaduna.
Kwamishinan 'yan sanda CP Ibrahim Adamu Bakori ya ce ba za a bar masu aikata laifi su samu mafaka ba, tare da yabawa jami’an da suka nuna jarumtaka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


