'Ku Tuba Kafin Ramadan': Dan Ta'adda Ya Gargadi Al'umma, Ya Fadi Matakin da Zai Ɗauka

'Ku Tuba Kafin Ramadan': Dan Ta'adda Ya Gargadi Al'umma, Ya Fadi Matakin da Zai Ɗauka

  • Wani kwamandan Boko Haram mai suna Mulwuta ya yi barazana ga mazauna Banki a Borno da ke Arewacin Najeriya
  • Dan ta'addan da ake zargin kwamandan Boko Haram ne ya ce dole mutanen yankin su tuba kafinn watan Ramadan ko a hallaka su
  • Barazanar ta haddasa fargaba a Banki, inda jama’a suka shiga damuwa, kasancewar garin ya sha fama da hare-haren ‘yan ta’adda a baya
  • Wani mazaunin Banki ya ce ko da Shekau yana raye da dakarunsa, bai iya yin komai a Banki ba, balle wannan yaro ƙarami

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Maiduguri, Borno - Wani da ake zargi kwamandan Boko Haram ne mai suna Mulwuta ya yi barazana ga mazauna Banki, wani gari a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.

A cewar wasu majiyoyi, dan ta’addan ya gargadi mutanen Banki cewa idan ba su "tuba" ba kafin Ramadan, za a "yanka su kamar awaki."

Kara karanta wannan

'Binani ce ta ci zaɓen Adamawa': Hudu Ari ya yi rantsuwa an tilasta shi game da Fintiri

Wani dan ta'adda ya gargadi mutane su tuba kafin Ramadan
Wani da ake zargin Kwamandan Boko Haram ne ya gargadi al'umma a Borno su tuba kafin Ramadan. Hoto: Legit.
Asali: Original

Boko Haram sun hallaka kwamandan sojoji

Hakan na kunshe ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Zagazola Makama ya wallafa a shafin X a yau Lahadi 9 ga watan Janairun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan gargadi ya biyo bayan wani mummunan hari da yan Boko Haram suka sake kai wa a sansanin soji na Malam-Fatori, inda suka kashe kwamandan soji, jami'ai biyu, da sauran sojoji.

Yan ta'addan sun kai harin ne da motocin yaki, suna kona gine-gine da motoci, tare da jikkata sojoji da kuma batan wasu.

Harin na zuwa ne bayan wani farmaki a Damboa, inda aka kashe sojoji da dama, yayin da wasu suka bata.

Dan ta'adda ya yi wa al'ummar Banki gargadi

Bayan gargadi dan ta'addan, mazauna yankin sun shiga fargaba kan wannan gargadi na dan ta'addan a yankin.

“Ko da Shekau yana raye da dukan mayakansa, bai iya yin komai a Banki ba, balle wannan yaro ƙarami. Kada kowa ya damu da shi.”

Kara karanta wannan

Dabara ta fara ƙarewa ƙasurgumin ɗan bindiga, sojoji sun koma maɓoyar Bello Turji

Cewar wani mazaunin yankin

Matakan Boko Haram sun hallaka al'umma

A baya, kun ji cewa wasu abubuwan fashewa sun tarwatse a hanya, tare da hallaka mutane biyu a kan hanyarsu zuwa kasuwar Garkida a Adamawa.

Yan sanda sun tabbatar da harin, sun ce mota dauke da yan kasuwar ta taka bam din da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka dasa.

Wani dan uwa wanda abin ya shafa, ya ce 'yan ta’adda na dasa bama-bamai a hanyoyin karkara da dare, a wani sabon salon kai hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.