Abdussalam: Nauyin kare Dadiyata da nemo shi ya na wuyan Gwamnatin Kaduna

Abdussalam: Nauyin kare Dadiyata da nemo shi ya na wuyan Gwamnatin Kaduna

Aminu Abdussalam Gwarzo, daya daga cikin jagororin Kwankwasiyya a Najeriya, ya sake yin magana game da bacewar Abubakar Idris ‘Dadiyata’.

Idan ba ku manta ba yau kusan kwanaki 400 kenan da wasu mutane da ba a sansu ba, su ka zo har gida su ka yi awon-gaba da Dadiyata, har yau babu labarinsa.

Gwamnatin jihar Kaduna ta fito ta bayyana cewa wannan Bawan Allah ba ya hannunta, kamar yadda wasu su ke zargi, hakan ya zo ne bayan shekara guda.

A wani shiri na ga fili ga mai doki, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya yi wa gwamnatin Kaduna ta Malam Nasir El-Rufai raddi, ya ce ita ke da nauyin kare mutane.

Aminu Abdussalam ya ce ya ji maganar da gwamnatin jihar Kaduna ta yi, wanda ta fito ne daga bakin babban lauyan gwamnati watau Atoni-Janar na jihar.

A cewar Abdussalam, gwamnatin Nasir El-Rufai ta kan yi magana ne ta ofishin kwamishinan yada labarai ko kuwa sakataren yada labarai na mai girma gwamna.

KU KARANTA: Ba mu tsare da Dadiyata - Gwamnatin Kaduna

Abdussalam: Nauyin kare Dadiyata da nemo shi ya na wuyan Gwamnatin Kaduna
Abdussalam, Dadiyata da Abba Gida-Gida
Asali: Facebook

Kwamred Abdussalam Gwarzo ya ce: “Ko ta ina aka biyowa maganar, Dadiyata a Kaduna aka sace shi, kuma wajibi ne na gwamnatin Kaduna su nuna damuwa, da kokari da hakilo na nemo inda ya ke.”

Ya ce bai dace “Gwamnati ta yi shiru ko burus’ game da lamarin ba inda har ta kai ana zargin cewa akwai hannunsu a dauke wannan matashi ba.

“Ai wajibin gwamnati ne da gwamna su nemo duk wanda ya ke cikin kasarsa da aka dauke shi ko iyalansa.” Abdussalam Gwarzo ya ce a Najeriya ne kadai za ayi irin haka.

‘Dan Kwankwasiyyar ya ce ko mutumin da ba kai darajar Dadiyata ba, bai kamata a dauke shi ba, balle kuma irin wannan fitaccen mutum, ‘dan gwagwarmayar kasa.”

‘Dan takarar na zaben 2019, ya ce rokonsu shi ne a gano wannan Bawan Allah, sannan ya ce kullum cikin taron addu’o’i su ke na ganin Ubangiji ya tona asirin miyagun.

Ya ce: “Rantsuwa gwamna ya yi cewa zai kare duk wanda ya ke cikin huruminsa. Dadiyata ya na ciki. Ina aka kwana?”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng