Bidiyon tsiraici: Maryam Booth ta bayyana gaskiyar lamari

Bidiyon tsiraici: Maryam Booth ta bayyana gaskiyar lamari

Fitaciyyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maryam Booth ta yi martani a kan bidiyon tsaraicinta da ke yawo a shafukan sadarwa.

Maryam ta fito ta karyata mawakin hip-hop Ibrahim Ahamad Rufa'i, wanda aka fi sani da Deezell, a kan ikirarin da ya yi na cewa ba ya da hannu wajen yada bidiyon nata.

A jiya Alhamis, 7 ga watan Fabrairu ne bidiyon mai tsawon sakan biyu ya ɓulla a soshiyal midiya inda aka ga fitacciyar jarumar ta Kannywood tsirara zigidir a wani daki.

A yau Juma’a kuma sai wasu kafafen soshiyal midiya su ka ambaci Deezell a matsayin wanda ya saki bidiyon don ya tozarta ta bayan soyayyar su ta rushe.

Nan da nan Deezell ya karyata zargin a wata sanarwa da ya bayar a Twitter da Instagram.

Bidiyon tsiraici: Maryam Booth ta bayyana gaskiyar lamari
Bidiyon tsiraici: Maryam Booth ta bayyana gaskiyar lamari
Asali: UGC

To amma Maryam ta karyata shi a cikin daren yau Juma’a, ta ce ba shakka shi ne ya dauki bidiyon ta a lokacin da ta ke kokarin saka tufafi.

KU KARANTA KUMA: Wani mutum ya fusata Nafisa Abdullahi akan bidiyon Maryam Booth

A cikin sanarwar da ta bayar a karon farko kan wannan badakala, wadda ta saka a shafukan ta na soshiyal midiya, Maryam Booth ta ce: "Ina sane da abubuwan da ke wanzuwa yanzu da kuma surutan da ake yi a kafafen yada labarai game da wani bidiyo da aka ce ni ce, aka yaɗa a kafofi da dama na soshiyal midiya, kuma dubban mutane su ka kalla.

"Da farko, na yi niyyar in yi shiru har sai jami'an tsaro sun kammala nazarin su da binciken su.

"Maganar da wani mutum mai suna Ibrahim Ahmad Rufa'i, wanda aka fi sani da sunan Deezell, ya yi, ita ta saka ni tilas in ce wani abu.

"A matsayi na na 'ya mace, 'yar wasa kuma wadda wasu ke kwaikwayo da ita, ba zan bari a shashantar da wannan maganar ba.

"A gaskiya, ina so in bayyana cewa shi wannan mutum (Ibrahim Ahmad Rufa'i) ya sha yi mani barazanar cewa zai saki bidiyon idan ban ba shi kudi ba.

"A matsayi na na 'ya mace, jarumar fim kuma wadda miliyoyin mutane ke koyi da ita, na yi ta kokarin na kare mutunci na ta kowace hanya da zan iya, amma kawai ba tare da sani na ba sai wannan bidiyo da ya shekara uku da ɗauka ya ɓullo.

"A yanayi irin wannan, tilas mutum ya tsaya ya yi karatun ta-nutsu kafin ya ce komai, amma gaskiya ne cewa Deezell tsohon saurayi na ne wanda kuma shi ne ya dauki hoton bidiyo na a lokacin da na ke saka kaya.

"A yanzu ina ta faman tuntubar abokan shawara ta don samun hanyar daukar matakin shari'a da ya dace kan dukkan wanda ke da hannu cikin al'amarin sakin wannan bidiyo.

"Ina godiya ga iyaye na da 'yan'uwa na da kawaye na da abokai na, da kuma musamman masoya na, saboda yadda su ka nuna tausayawa a gare ne a wannan mawuyacin hali. Na gode maku baki daya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel