Yadda Aka Yi Bidiyon Surar Jikina Ya Fita Har Aka Koreni A Harkar Fim - Safara’u Kwana Casain

Yadda Aka Yi Bidiyon Surar Jikina Ya Fita Har Aka Koreni A Harkar Fim - Safara’u Kwana Casain

  • Dakatacciyar jarumar fina-finan Hausa, Safiyya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u ta shirin Kwana Casa'in ta magantu kan bayyanar bidiyon da ya yi sanadiyar sallamarta
  • Safa ta ce ita ta yi bidiyon ne don nishadantar da kanta inda wani da bata sani ba ya fitar da shi daga wayanta
  • Mawakiyar ta ce sabanin tunanin da ake yi cewa ita yar madigo ce ko saurayi ta turawa ya fitar sam ba haka abun yake ba, daga wayarta ne wani na kusa da ita ya fitar da shi

Najeriya - Korarriyar jarumar nan ta masana’antar shirya fina-finan hausa, Safiyya Yusuf wacce aka fi sani da Safara’u ta shirin Kwana Casa'in ta magantu a kan sallamarta da kamfanin Arewa 24 ta yi.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 3 Da Aure Ba Tare Da Sun Ga Juna Ba, Yar Najeriya Ta Hadu Da Baturen Mijinta A Amurka

Safa kamar yadda ake kiranta a yanzu ta bayyana cewa wasu na kusa da ita ne suka fitar da bidiyon domin ta kan yi su ta ajiye a cikin wayarta idan tana jin nishadi.

Safiyya Yusuf
Yadda Aka Yi Bidiyon Surar Jikina Ya Fita Har Aka Koreni A Harkar Fim - Safara’u Kwana Casain Hoto: safarau_safa
Asali: Instagram

Tsohuwar jarumar wacce ta zama mawakiya a yanzu ta kuma bayyana cewa farkon faruwar abun sai da ta kwashe tsawon watanni uku bata fita ba saboda kunyan mutane.

A hira da ta yi da sashin Hausa na BBC, Safa ta ce ta fuskanci tarin kalubale tare da la’anta a wajen mutane wadanda suka yi zargin cewa ita yar madigo ce ko kuma saurayi ta turawa ya fitar da shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hakazalika ta ce ya kai har wani ya jefeta da dutse a layinsu wata rana da ta fito waje, kuma cewa haka ake ta tsine mata a shafukan soshiyal midiya har ta kusa share shafukanta na Instagram, TikTok da sauransu.

Kara karanta wannan

Tsoffin Maza Sun Fi Iya Soyayya: Matashiya Yar Shekaru 30 Da Ta Auri Dan Shekaru 80

Sai dai kuma, Safa ta ce ta dawo daidai ne bayan iyayenta da danginta sun karfafa mata gwiwa tare da nusar da ita cewa hakan kaddara ce a rayuwarta, kuma ga shi a yanzu komai ya wuce.

Kalli bidiyon hirar tasu a kasa:

Jama'a sun yi martani

young_ustaax ya yi martani:

"Tabbas Iblis na yayin ki yan mata. I just wish akwai yadda zamu iya fadan magana ta kai zuciyan ki . Bari muga nan da shekara goma zuwa ashirin me zai faru . Allah shi kyauta . Allah ka shirya mu baki daya. Ya shirya mana zuri’a ."

maryaaamah_ ta ce:

"Fun manya,Allah ya shiryeki damu amin summa amin."

umaraeeshartu ta ce:

"Wai fun wato a ajiye tsiraici Chb Allah y kyauta."

ammas_confectionery ya ce:

"Allah Ubangiji Ya shirya."

Burina Na Zama Babbar Attajira Sunana Ya Danne Na Dangote – Maimuna Wata Yarinya

A wani labarin, Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Maimuna Muhammad wacce aka fi sani da ‘Wata Yarinya’ ta bayyana babban burinta a rayuwa.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wani ya yi aikin dana sani, ya kashe masoyiyarsa saboda katin ATM

A cewar matashiyar jarumar wacce take haifaffiyar yar Maiduguri burinta shine ta zama babbar attajira kuma yar kasuwa.

Ta ce za ta so ace duniya ta santa a wannan fage na kasuwanci ta yadda zai kai sunanta ya danne na mai kudin Afrika kuma shahararren dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote.

Asali: Legit.ng

Online view pixel