'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wata Fitacciyar Jami'a a Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wata Fitacciyar Jami'a a Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wasu rahotanni da ake yadawa a kafafen sada zumunta sun nuna cewa 'yan bindiga sun kai kazamin hari kan dalibai a Jami'ar Summit da ke Kwara
  • Hukumar makarantar ta fito ta musanta wannan labari, inda ta bayyana shi a matsayin tsagwaron karya mara tushe
  • Ta bukaci iyaye da sauran al'umma su kwantar da hankulansu domin Jami'ar na cikin kwanciyar hankali, ta gargadi masu yada jita-jitar harin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Offa, jihar Kwara - Rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki Jami'ar Summit da ke garin Offa a jihar Kwara ba gaskiya ba ne.

Hukumomin jami'ar wacce ke a shiyyar Arewa ta Tsakiya a Najeriya, sun musanta wannan jita-jita da ake yadawa, suna mai cewa labarin kanzon kurege ne.

Kara karanta wannan

Ana barazanar hana ADC taro a Abuja, Atiku ya fadi matakin da za su dauka

Jami'ar Summit.
Babbar kofar shiga Jami'ar Summit da ke garin Offa a jihar Kwara Hoto: News Bulletin
Source: Facebook

Da gaske an kai hari jami'ar Summit?

A rahoton Leadership, jami’ar Summit da ke Offa a Jihar Kwara ta karyata rahotannin da ke yawo cewa ‘yan bindiga sun kai hari harabar makarantar.

Shugaban jami’ar (VC), Farfesa Abiodun Musa Aibinu, ya shaida cewa duk da sanarwar da makarantar ta fitar a baya don karyata rahoton, har yanzu labarin na karya na ci gaba da cin kasuwa kafafen sada zumunta.

Ya ce jita-jitar ta fara ne kwanaki da suka gabata inda aka fara yadawa a hankali a yanar gizo, kafin daga bisani a ranar 1 ga watan Afrilu, 2026, labarin ya sake bayyana da karfi, har ya bazu sosai a dandalin sada zumunta.

A cewarsa, sakonni sun yadu a dandalin WhatsApp, mutane suka fara yada labarin, lamarin da ya haifar da fargaba tsakanin iyaye da dalibai, inda wasu suka fara daukar labarin a matsayin gaskiya.

Wane hali ake ciki a Jami'ar Summit?

Kara karanta wannan

Jagoran 'yan bindiga ya tura sako ga gwamnati, ya fadi matsayar sulhun da aka yi a Katsina

Sai dai Farfesa Aibinu ya jaddada cewa babu wani harin yan bindiga da aka kai jami’ar, yana mai cewa makarantar ta fito karara ta karyata wannan rahoto tun farko, tare da bayyana shi a matsayin labari marar tushe.

Ya tabbatar da cewa jami’ar na cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, tana ci gaba da gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, kuma babu wata matsalar tsaro da aka samu.

Shugabannin makarantar sun ce suna binciken inda labarin ya samo asali, tare da gargadin cewa za a dauki mataki kan duk wanda aka samu da hannu wajen yada wannan jita-jita.

Jihar Kwara.
Taswirar jihar Kwara da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Shugaban jami'a ya gargadi 'yan Najeriya

A karshe, ya gargadi jama’a da su guji yada bayanan da ba a tabbatar da su ba, yana mai cewa yin haka na kara dagula al’amura.

Ya kara da cewa ilimi na gaskiya yana bukatar hakuri da zurfin tunani, tare da tabbatar da sahihancin labari kafin yada shi ga jama’a, kamar yadda shafin News Bulletin ya wallafa a Facebook.

Yan bindiga sun sace ciyaman a jihar Delta

A wani labarin, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Sapele, Hon. Bright Abeke da ke jihar Delta.

Kara karanta wannan

Tsaro ya damalmale, Amnesty ta fadi yawan mutanen da aka sace a watanni 3

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindigar sun yi nasarar tafiya da shugaban karamar hukumar ne bayan sun yi musayar wuta da jami'an tsaronsa.

Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta sun datse manyan hanyoyin shiga da fita na garin Sapele da ke Karamar Hukumar Sapele da shingayen bincike domin ceto shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262