Mutane Sun Shiga Kunci da Aka Dauke Sabis din Waya a Kananan Hukumomi 4 a Najeriya

Mutane Sun Shiga Kunci da Aka Dauke Sabis din Waya a Kananan Hukumomi 4 a Najeriya

  • Alamu sun nuna cewa kamfanonin sadarwa sun dauke sabis din waya a kananan hukumomi hudu na Arewacin jihar Zamfara
  • Mazauna yankin sun bayyana halin da suka tsinci kansu tsawon watanni uku babu sabis din MTN, Airtel da kuma Glo
  • Sun roki hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) ta kawo masu agaji ta hanyar tilasta dawo masu da harkokin sadarwa yadda aka saba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Al’umma daga mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa sun yi kira ga Hukumar Sadarwar Najeriya (NCC) da ta gaggauta dawo da sabis din sadarwa da aka dauke tsawon watanni uku a yankin.

Dauke sabis din waya a kananan hukumomi hudu da ke mazabar Sanatan Zamfara ta Arewa ya jefa jama'a cikin kunci, inda suka fara kira ga NCC ta kawo masu dauki.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun yi dirar mikiya a kan mazauna Zamfara, sun kashe mutane

Karfen dadarwa.
Hoton ma'aikata a wurin turken sadarwa a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wannan kira ya fito ne daga kungiyar Kaura Namoda Focus Forum (KNFF) ta bakin mai magana da yawunta, Abdulrazak Bello, in ji rahoton Premium Times.

Wane kananan hukumomi ne aka dauke sabis?

A cewarsa, an katse sabis a kananan hukumomin Birnin Magaji, Kaura Namoda, Shinkafi da Zurmi, wanda ke da yawan jama’a sama da miliyan 1.78

Ya jaddada cewa tun watanni uku da suka shige, aka dauke sabis din MTN, Airtel da Glo ba tare da wani karin bayani ga masu amfani da layukan kamfanonin ba.

Abdulrazak Bello ya ce rufe layukan sadarwar ya durkusar da harkokin kasuwanci da na ilimi a yankin.

Ya nuna cewa akwai makarantu da cibiyoyin kasuwanci irin su Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda, kasuwannin Shinkafi da Kasuwar Daji da ke hada ‘yan kasuwa daga ciki da wajen ƙasa.

Halin da mutanen Arewacin Zamfara ke ciki

“Allah Ya albarkace mu da matasa masu sana'o'in zamani da kasuwancin intanet a yankin Zamfara ta Arewa, amma katse sabis ya jefa su a damuwa, wasu sun fara hijira, lamarin da ka iya haifar da rashin tsaro,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Wasu ma'aikata sun jawo wa kansu, gwamna ya kore su daga aiki nan take

Wasu mazauna yankin sun roki NCC ta yi amfani da dokar sadarwa ta Najeriya (NCA) ta 2003 wajen tilasta wa kamfanonin sadarwar su dawo da sabis.

“Masu amfani da layi suna da hakkin samun sabis mai inganci da kuma bayani a kowane lokaci idan aka samu matsala, amma an yi shiru tsawon watanni,” in ji su.
Hukumar NCC.
Hoto hedkwatar hukumar sadarwa ta kasa (NCC) da ke Abuja Hoto: NCC
Source: Twitter

Kasuwanci ya fara durkushewa a yankuna 4

Wani dan kasuwa, Umar Kaura, ya ce rashin sadarwa ya rage yanayin walalwala da jin dadin rayuwa a yankin, cewar ruwayar Vanguard.

"Ba mu iya samun bayanai ta intanet, kasuwancinmu ya tsaya cik saboda ba mu iya yin odar kaya daga Kano ko Lagos kamar da,” in ji shi.

Kokarin jin ta bakin kakakin NCC, Nnena Ukoha, bai yi nasara ba, domin ba ta amsa kira da sakonnin waya da aka tura mata ba.

Kamfanonin sadarwa sun hango matsala

A wani labarin, kun ji cewa kamfaninin sadarwa sun yi gargadin cewa matukar ba a magance hare-hare kan turakan sadarwa ba, za a iya fuskantar matsalar sabis a jihohi.

Kamfanonin sun buƙaci dakarun tsaron Najeriya su taimaka wajen kare turakan sadarwa domin gujewa rashin karfin intanet da ɗaukewar sabis.

Ƙungiyar manyan kamfanonin sadarwa ta kasa wato ALTON, ta nuna damuwa ƙwarai kan yadda sata da lalata kayayyakin sadarwa ke ƙaruwa a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262