Badaƙalar N19.4bn: An Samu Matsala Yayin Gurfunar da Ministan Buhari da Ɗan Uwansa a Kotu

Badaƙalar N19.4bn: An Samu Matsala Yayin Gurfunar da Ministan Buhari da Ɗan Uwansa a Kotu

  • Hukumar EFCC ta gamu da matsala yayin gurfanar da Hadi Sirika da ɗan uwansa a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja
  • An tsara fara sauraron shari'ar tsohon ministan kan tuhumar karkatar da kudin kwangila N19.4bn amma bai samu halarta ba saboda kuskuren EFCC
  • Lauyan hukumar yaƙi da rashawa ya shaidawa alkalin kotun cewa EFCC ta manta ba ta aika takardar sababbin tuhume-tuhume ga Sirika da ɗan uwansa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - An gamu da cikas a shirin gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da ɗan uwansa kan sabuwar baɗaƙalar kwantiragi ta N19.4bn.

An samu matsalar ne sakamakon waɗanda ake tuhuma, Sirika da ɗan uwansa ba su samu damar halartar zaman kotun ba ranar Talata kuma sun bar birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame harabar kotu ana cikin shari'a, sun kama mutum 2

Hadi Sirika da EFCC.
EFCC fa gamu da cikas a shirin gurfanar da Hadi Sirika da ɗan uwansa Hoto: Hadi Sirika, OfficialEFCC
Asali: Facebook

Lauyan hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC), Oluwaleke Atolagbe, ya faɗawa kotun cewa hukumar ba ta sanar da tsohon ministan da ɗan uwansa batun ƙarar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadi Sirika: EFCC ta ɗauki laifin kuskure

Rahoton Channels tv ya nuna cewa bisa haka lauyan EFCC ya roƙi alkalin kotun mai shari'a Suleiman Belgore, ya ɗage zaman zuwa wani lokaci kuma ya amince.

Daga nan sai mai shari'a Belgore ya sanya ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu, 2024 domin gurfanar da waɗanda ake tuhumar da wawure kuɗi N19.4bn.

Zargi da EFCC take yi wa Sirika

A wannan karon, hukumar EFCC na tuhumar tsohon Ministan da dan uwansa da aika laifuffuka takwas da suka shafi almundahanar Naira biliyan 19.4.

An tattaro cewa waɗannda kuɗin na wasu kwangilolin ma’aikatar sufurin jiragen sama ne da tsohon ministan ya baiwa kamfanin Enginos Nigeria mallakin kaninsa Abubakar.

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da Ministan Buhari da ɗan uwansa a kotu kan tuhume-tuhume 8

A makon jiya, ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu, EFCC ta fara gurfanar da Hadi Sirika da ɗiyarsa Fatima da sirikinsa kan zargin karkatar da N2.7bn na kwantiragi.

Amma ba su amsa laifin da ake tuhumarsu a kai ba kuma kotun ta ba da belin kowanen su kan N100m da kuma wasu sharuɗɗa, The Nation ta ruwaito.

DSS ta kai samame kotu a Ogun

A wani rahoton kun ji cewa jami'an DSS sun kutsa kai cikin kotu ana cikin shari'a, sun tafi da mutum biyu da ake tuhuma a jihar Ogun ranar Talata.

Lamarin dai wanda ya keta doka ya haifar da hayaniya a harabar kotun, inda lauyan waɗanda ake tuhuma ya caccaki danyen aikin ma'aikatan DSS.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel