Sarkin Nufawa da Sanata David Umaru sun zargi gwamna Bello da nuna bangarenci da rashin iya shugabanci

Sarkin Nufawa da Sanata David Umaru sun zargi gwamna Bello da nuna bangarenci da rashin iya shugabanci

- Etsu Nupe ya ce rashin iya shugabancin gwamna Sani Bello ya sa talauci ya mamaye jihar Neja

- Sanata David Umaru ya ce bai kamata gwamnan jihar Neja ya rika maganar tazarce ba saboda bai tsinanawa jihar komai ba

Shugaban sarakunanan gargajiya na jihar Neja, Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, ya zargi gwamnatin, Abubakar Sani Bello, da nuna bangarenci da rashin iya shugabanci.

Ya ce gwamnatin jihar Neja na yanzu, na ‘yan uwa da abokan arziki ne kawai ban na mutanen jihar ba. Burin shine suga al’ummar jihar suna cikin wahala.

Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da gamayyar kungiyoyin kabilun jihar Neja mai suna Gbapeko, suka kawo masa ziyara a fadar sa na Bida.

Etsu Nupe da Sanata David Umaru sun zargi gwamna Bello da nuna bangarenci da rashin iya mulki
Etsu Nupe da Sanata David Umaru sun zargi gwamna Bello da nuna bangarenci da rashin iya mulki

Sarkin ya bayyana takaicin sa akan rashin cigaba da jihar take fama da shi a karkashin gwamnatin, Sani Bello.

KU KARANTA : An shiga rundani a jihar Legas yayin da wasu 'yan ta'ada suka kashe wani dalibi da ma’akaicin jami’an Legas

A jawabin da Wamban Nupe, Mahmud Abubakar, yayi a madadin Etsu Nupe, ya ce duka manyan hanyoyin jihar sun lalace, ga talauci ya mamaye mutanen jihar kuma gwamnatin jihar tana siyasantar da al’amarin.

Shima sanata mai wakiltar mazabar kudancin jihar Neja, David Umaru, ya soki gwamnan jihar Neja akan rahshin iya shugabancin sa.

Umaru ya ce, bai kamata, Gwamna Sani Bello, ya rika maganar tazarce ba saboda babu takamammen abun da ya tsinanawa mutanen jihar Neja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng