Gwamna Ganduje yayi sabbin nade-nade masu muhimmanci a gwamnatinsa

Gwamna Ganduje yayi sabbin nade-nade masu muhimmanci a gwamnatinsa

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya amince da nadi da sake nadin wasu shugabannin hukumomin gwamnati a jihar.

Babban sakataren labaran gwamnan, Malam Abba Anwar ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya saki a ranar Talata, 16 ga watan Yuli a Kano.

Daga cikin wadanda aka nada sun hada da Sheikh Abdalla Pakistan a matsayin Shugaban hukumar kula da jin dadin mahajattan jihar Kano da kuma Dr Aliyu Musa a matsayin Darakta-Janar na hukumar Hisbah a jihar.

Anwar ya bayyana cwa an nada Dr Halima Rabi’u Abdullah a matsayin babbar sakatariyar hukumar ilimi da kuma Alhaji Gali Sadiq a matsayin Manajan Darakta na kamfanin Radiyo na jihar Kano.

A cewarsa, gwamnan ya kuma sake nada Dr Ibrahim Bichi a matsayin babban sakataren dakin karatu na jihar Kano da kuma Sagir Sadisu Buhari a matsayin Darakta-Janar na hukumar bincike.

An kuma sake nada Lawan Sabo a matsayi n Manajan-Darakta na kamfanin buge-bugen takardu, Sa’a Ibrahim Manajan Darakta na Abubakar Rimi Television (ARTV), Dr Hibrilla Mohammed Manajan Darakta na KSIP.

KU KARANTA KUMA: Buhari ma babban dan adawar Obasanjo ne a baya – Shehu Sani ya waiwayi tarihi

Sauran sun hada da Alhaji Ibrahim Galadima, Shugaban kungiyar wasanni na Kano da kumaMista Sakina Yusuf a matsayin Shugaban kotun kula da harkokin Hajji na jihar Kano.

Gwamnan ya yaba ma wadanda aka sake ba mukami kan isar da ayyukansu da suka yi da kyau a mulkinsa na farko sannan yayi kida da dukkanin wadanda aka ba mukamai das u ci gaba da sauke hakkokin da ke kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel